Abin da zan yi a matsayin sabon IGP - Mohammed Adamu
- Sabon Sufeta Janar na 'yan sanda, Mohammed Adamu ya bayyana abubuwan da zai fara aiwatarwa da zarar ya kama aiki
- Shugaban 'yan sandan ya ce zai dora daga inda tsohon shugaban ya tsaya kuma zai bullo da sabin tsare-tsare domin magance kallubalen tsaro da aka fama dashi a kasar
- Ya kuma ce zai yi biyaya ga doka wurin aiwatar da ayyukansa ba tare da nuna fifiko ga wani bangare ba
Sabon Sufeta Janar na rundunar 'yan sandan Najeriya, Abubakar Mohammed Adamu ya ce zaiyi biyaya ga doka wajen gudanar da ayyukan tsare lafiya da dukiyoyin al'umma.
A hirar da ya yi da manema labarai a gidan gwamnati bayan ganawar da ya yi da Shugaba Muhammadu Buhari da tsohon Sufeta Janar, Ibrahim Idris, Adamu ya ce zai yi aiki tukuru domin magance kallubalen tsaro da ke addabar kasar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Twitter
DUBA WANNAN: Legas: An kama manyan 'yan kasuwa dake daukar nauyin 'yan bindigar Zamfara
Ya shaidawa manema labarai cewa: "Mun san cewa akwai wasu kallubalen tsaro da ya kamata mu magance a kasar; Garkuwa da mutane, satan mutane da wasu matsalolin tsaro. Daga tsare-tsaren da tsohon IGP ya yi, zamu sake sabbin tsare-tsare domin ganin mun magance wadannan matsalolin.
"A kan batun zabe kuma, kun ji tsohon Sufeta Janar ya ce an kammala shiri domin gudanar da sahihiyar zabe a dukkan sassan Najeriya. Zamu dora daga inda ya tsaya domin tsara yadda za a gudanar da zabe cikin zaman lafiya da lumana a kasar.
"Mu kwararu ne saboda haka za muyi biyaya ga doka kuma za muyi abinda ya dace. Ba zamu karya dokokin aikin mu; zamu bawa dukkan 'yan siyasa damar da doka ta basu domin su gudanar da siyarsu."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng