Muna son biyan N30,000 a matsayin mafi karancin albashi amma akwai wata matsala - Gwamnonin Najeriya

Muna son biyan N30,000 a matsayin mafi karancin albashi amma akwai wata matsala - Gwamnonin Najeriya

- Har yanzu maganar batun karin albashin ma'aikata na cigaba da tayar da kura a tsakanin kungiyar kwadago da bangaren zartarwa

- Kungiyar kwadago ta ce zata yi wani babban gangami a watan Janairu domin kara jaddada aniyarta na babu-gudu-babu-ja-da-baya a kan kara wa ma'aikata albashi

- Ana zargin cewar rashin amincewar gwamnonin jihohin Najeriya ne babban cikas ga batun karin albashin

Kungiyar gwamnoni Najeriya (NGF) ta ce gwamnonin kasar nan na son biyan N30,000 a matsayin mafi karancin albashi amma halin tsananin da tattalin arzikin kasa da jihohi ke ciki ne ke dakatar da su.

Abdulrazaque Bello Barkindo, shugaban sashen yada labarai na NGF, ne ya sanar da hakan yau, Litinin, a Abuja.

Barkindo ya ce matsalar kudi da wasu matsalolin da jihohi da dama ke fuskanta ne ya sa ba zasu iya biyan mafi karancin albashi na N30,000 ba.

Muna son biyan N30,000 a matsayin mafi karancin albashi amma akwai wata matsala - Gwamnonin Najeriya

Gwamnonin Najeriya
Source: Twitter

Ya ce yin bayani ya zama wajibi saboda kalaman sakataren kungiyar kwadago, Peter Eson, dake bayyana cewar gwamnoni ne basa son yin karin albashin yayin wata hira da aka yi da shi.

Ya kara da cewar batun cewar gwamnoni ne basa son yin karin albashin ba gaskiya bane kuma yunkuri ne na ingiza jama'a.

DUBA WANNAN: APC zata sha kaye a jihohi da yawa - Murtala Nyako

Kazalika ya bayyana cewar gwamnonin sun yi tayin kara albashi daga N18,000 zuwa N22,000 bayan kwamitin da aka kafa a kan karin albashi ya mika rahotonsa a ranar 6 ga watan Oktoba.

"Gwamnonin sun bayyana cewar zasu iya biyan N22,000 a matsayin mafi karancin albashi, amma hakan ba yana nufin jiha ba zata iya biyan fiye da haka ba. Duk jihar da take da sukuni zata iya biyan fiye da haka, amma N22,000 shine mafi karancin albashi da gwamnonin suka amince da shi bayan doguwar tattaunawa a tsakaninsu," a cewar Barkindo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel