Da duminsa: Mayakan Boko Haram ba su kwace garin Baga ba - Hukumar Sojin Najeriya

Da duminsa: Mayakan Boko Haram ba su kwace garin Baga ba - Hukumar Sojin Najeriya

Hukumar Sojin Najeriya ta ce ba gaskiya bane cewa mayakan Boko Haram sun kwace garin Baga duk da cewa har yanzu ana gwabzawa tsakanin sojoji da mayakan Boko Haram a garin.

Shugaban bayar da horo da ayyuka na soji, Manjo Janar Lamidi Adeosun ne ya bayarda wannan sanarwar a taron manema labarai da ya kira a hedkwatan Operation Lafiya Dole a Borno.

Wannan sanarwar ta hukumar sojin yana zuwa ne a lokacin da wasu rahotanni ke yaduwa na cewa mayakan kungiyar Boko Haram na sashin Albarnawi sun kwace garin Baga a jihar Borno.

Da duminsa: Mayakan Boko Haram ba su kwace garin Baga ba - Hukumar Sojin Najeriya
Da duminsa: Mayakan Boko Haram ba su kwace garin Baga ba - Hukumar Sojin Najeriya
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Wani da ya yiwa kanwarsa mai shekaru 15 ciki a Kano ya dora laifi kan shaidan

A baya, an ruwaito cewa wani jami'in sojan ruwa ya rasa ransa yayin artabu da sojoji su kayi da 'yan ta'addan kungoyar Boko Haram a hedkwatar jami'an tsaron hadin gwiwa ta MNJTF a Baga na jihar Borno.

A ranar Laraba, hukumar sojin Najeriya ta ruwaito cewa dakarun sojin suna fafatawa da 'yan ta'adda a Baga sai dai ba a bayar da cikakken bayanin abinda ke faruwa ba.

A wata sanarwa da Brig. Janar Kukasheka Usman ya fitar a ranar Alhamis, ya ce dakarun sojin Najeriya ta takwarorinsu na sojin ruwa fafata da mayakan Boko Haram cikin daren Alhamis.

Mai magana da yawun sojin ya ce, dakarun soji na Operation 3 na Lafiya Dole suna cigaba da artabu da 'yan ta'addan.

Ya kuma ce jami'an sojojin sama sun fara yiwa mayakan na Boko Haram luguden wuta a yayin da suke kokarin tserewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel