Saraki da Dogara sunyi tsokaci kan kisar gillar da aka yiwa Alex Badeh

Saraki da Dogara sunyi tsokaci kan kisar gillar da aka yiwa Alex Badeh

- Shugabanin majalisun tarayya Bukola Saraki da Yakubu Dogara sunyi tsokaci a kan kisar gillar da aka yiwa tsohon shugaban tsaro, Alex Badeh

- Bukola Saraki ya ce rasuwarsa babban rashi ne ga kasa kuma ya mika sakon ta'aziyarsa da iyalan mamacin da hukumar soji

- Yakubu Dogara kuma ya bayyana ya ce abin bakin ne ya faru kuma ya yi fatan za a binciko wadanda suka aikata kisar tare da hukunta su

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya bayyana jimaminsa a kan kisar gillar da aka yiwa tsohon babban hafsan tsaron na Najeriya, Alex Badeh a jiya inda ya ce mutuwarsa babban rashi ne da Najeriya.

Rahotanni sun ce an kashe shi ne a hanyar Abuja zuwa Keffi yayin da ya ke hanyarsa ta komawa gida daga gona. Ya mutu ne a cikin motarsa.

DUBA WANNAN: Sojoji sun ragargaji 'yan ta'addar Zamfara, hotunan wadanda suka mutu

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Saraki ya ce: "Najeriya ta sake yin babban rashi sakamakon rasuwar tsohon babban hafson tsaro, Air Cif Marshal Alex Badeh. Ina mika ta'aziya da iyalansa da hukumar soji. Allah ya jikansa da rahama, Amin."

Kazalika, shima Kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara ya ce kashe tsohon shugaban tsaron na kasa abin bakin ciki ne da tayar da hankali.

"Labarin da na samu na gisar gillar da aka yiwa tsohon babban hafson tsaro, Air Cif Marshal Alex Badeh abin bakin ciki ne da tsaro. Ina mika ta'aziya ta ga iyalana da masoyansa, kuma ina fatan za a gano wadanda suka aikata abin a kuma hukunta su."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel