Hotunan taransifoma 50 da gwamnatin Kaduna za ta rabawa unguwanni da garuruwa

Hotunan taransifoma 50 da gwamnatin Kaduna za ta rabawa unguwanni da garuruwa

Gwamnatin jihar Kaduna, karkashin jagorancin Malam Nasir El-Rufa'i, ta sayo na'urar bayar da wutar lantarki, ma su girman 500KVA da 300KVA, guda 50 domin rabawa ga garuruwa da unguwanni 50 da ke fadin jihar.

Ma'aikatar raya karkara da birane ta jihar Kaduna ce ta sanar da hakan a shafinta na Facebook, a yau, Litinin.

Ma'aikatar ta bayyana cewar, a cikin shekaru biyu da su ka wuce, gwamna El-Rufa'i ya raba tare da dasa taransifoma fiye da 108 a fadin jihar.

Kazalika ta bayyana cewar gwamnan ya gudanar da aiyukan ba tare da sanarwa ko gayyatar jama'a ba.

Hotunan taransifoma 50 da gwamnatin Kaduna za ta rabawa unguwanni da garuruwa

Hotunan taransifoma 50 da gwamnatin Kaduna za ta rabawa unguwanni da garuruwa
Source: Facebook

Hotunan taransifoma 50 da gwamnatin Kaduna za ta rabawa unguwanni da garuruwa

Hotunan taransifoma 50 da gwamnatin Kaduna za ta rabawa unguwanni da garuruwa
Source: Facebook

A wani labarin na Legit.ng, kun ji cewar jirgin kasa ya mirtsike wani mutum mai matsakaicin shekaru, da ya zuwa yanzu ba a gano ko waye ba, a yankin Phikwore da ke unguwar Kubwa a birnin tarayya, Abuja.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya rawaito cewar matashin ya bar wata takarda kafin daga bisani ya je ya kwanta a kan diga domin jirgin kasa ya bi ta kansa.

NAN ta bayyana cewar lamarin ya faru ne a yau, Litinin, da misalin karfe 12:45 na rana.

DUBA WANNAN: Tsohon gwamnan PDP ya musanta mallakar manyan kadarori da EFCC ta bankado a Kaduna

Matashin ya bar wasika a cikin wata jakarsa da ya ajiye a gefen digar jirgin da ya kwanta.

Wasu shaidun gani da ido da su ka yi magana da NAN sun ce matashin ya bar rubutaccen sako ga matar sa da yaransa kamar haka; "ku yafe min, saboda bani da kudin da zan iya daukar nauyin ku."

Ya zuwa yanzu dai ba a iya gano suna ko daga inda mutumin ya fito ba.

Kakakin hukumar kula da harkokin jirgin kasa, Mista Niyi Ali, ya tabbatar da faruwar lamarin ga NAN tare da bayyana cewar har yanzu suna binciken dalilin mutumin yin abinda ya aikata.

"Za mu yi bincike domin gano abinda zai sa matashi ya kwanta a titin jirgin kasa domin ya bi ta kansa, ya mutu," a cewar Ali.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel