Gwamnatin jihar Borno ta bawa sojoji 5 kyautar manyan motoci, hotuna

Gwamnatin jihar Borno ta bawa sojoji 5 kyautar manyan motoci, hotuna

Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, ya kaddamar tare da mika makullan motoci ga wasu jami'an soji 5 da su ka nuna bajinta a aikinsu na hidimtawa kasa.

Gwamnan ya mika makullan motocin ga jami'an sojin ne yayin da ya halarci taron rundunar soji na shekarar 2018 da aka gudanar a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Gwamnatin jihar Borno ta bawa sojoji 5 kyautar manyan motoci, hotuna
Gwamnatin jihar Borno ta bawa sojoji 5 kyautar manyan motoci
Asali: Twitter

Laftanal janar Tukur Yusuf Buratai, shugaban rundunar soji ta kasa, ne ya jagoranci taron na wannan shekarar kamar yadda dokar taron ta tanada.

DUBA WANNAN: Sakon Buhari ga shugabannin kasashen gefen tekun Chadi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya bude taron na wannan shekarar a ranar Laraba, yayin da ya kai ziyarar jaje da ta'aziyya ga dakarun soji da ke aikin tabbatar da zaman lafiya a jihar Borno biyo bayan wani mummunan hari da mayakan kungiyar Boko Haram su ka kai kan sansanin soji da ke garin Metele, karamar hukumar Guzamala, mai makwabtaka da kasar Chadi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel