An girke runduna runduna na jami’an tsaro a Maiduguri saboda ziyarar Buhari
An tsaurara matakan tsaro a garin Maiduguri da kewaye yayin da ake tsimayin ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai a yau Laraba 28 ga watan Nuwamba don kaddamar da taron manyan hafsan Sojoji da babban hafsan sojan kasa ya shirya.
Legit.com ta ruwaito wannan ne karo na farko da shugaba Buhari zai halarci taron wanda ake shiryashi sau hudu a shekara, bayan duk watanni uku. Ana shirya taron ne don yin nazari tare da duba ga ayyukan da rundunar Sojan kasa ta gudanar.
KU KARANTA: Yadda Kaakakin majalisa ya tsallake rijiya da baya a farfajiyar majalisa
Wannan taro na baiwa Sojojin damar duba nasarorin da suka samu, tare da kwatantasu da koma bayan da suka samu a yayin gudanar da ayyukan, ta haka ne zasu gano sabbin dabarun da ya kamata su bi wajen shawo kan matsalolin a gaba.
Haka zalika ana sa ran shugaba Buhari zai yi amfani da daman wannan ziyara da zai kai jahar Borno don kaima Sojojin dake bakin daga ziyara, inda zai tattauna dasu don jin halin da suke ciki, bukatunsu da kuma matsalolin da suke fuskanta a yaki da yan Boko Haram.
Bugu da kari Buhari zai gana da al’ummar jahar orno domin ya tabbatar musu da shirin gwamnatinsu bisa kokarin da take yi wajen kawo karshen ayyukan ta’addanci a jahar, da ma yankin Arewa maso gabas gaba daya.
Ana fatan wannan ziyara ta shugaban kasa zata kara ma Sojoji kwarin gwiwa, bayan harin da mayakan Boko Haram suka kai musu, inda suka kashe Sojoji da dama, har ma suka daura hotunan a yanar gizo.
Tun da fari dai anyi shirin gudanar da wannan taro ne a garin Bini na jahar Edo, toh amma sakamakon harin da yan ta’adda suka kai, sai shugaba Buhari ya nemi a sauya wurin taron zuwa garin Maiduguri.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng