Boko Haram sun kashe manoma 9, sun sace wasu mutane 12 a Borno
Mayakan kungiyar Boko Haram sun kashe manoma tara kuma sun sace wasu mutane 12 a wani kauye da ke Arewa maso gabashin jihar Borno kamar yadda mazauna kauyen suka shaidawa AFP.
A ranar Litinin, sun kawo farmaki a wasu gonaki da ke bayan kauyen Mammanti inda suka budewa manoman wuta suka kashe tara sannan suka jikkata guda uku.
"Mun samu gawar mutane 9 bayan harin," a cewar hakimin kauyen, Muhammad Mammanti.
"Yan ta'addan sun sace mutane 12 cikinsu har da mata sannan sun sari mutane uku da suka yi musu gardama yayin da su kayi niyyar tafiya da su," inji Mammanti.

Asali: UGC
Mayakan kungiyar na Boko Haram sun taho a kan keke kamar yadda wani manomi mai suna Usman Kaka da ya tsira da ransa ya ce.
DUBA WANNAN: An sako Buhari a gaba a kan satar basira a salon kamfen dinsa
"Kawai sun bude mana wuta ne a yayin da mu kayi kokarin guduwa," inji Kaka.
"Daga baya da muka dawo mun tsinci gawawaki tara da kuma mutane uku da aka sara da adduna a kawunansu saboda sun ki amincewa su tafi tare da yan ta'addan," inji shi.
A makon da ya gabata, mayakan Boko Haram din sun kai hari a kauyen Mammanti inda suka kashe mutum guda kuma suka kone gidaje masu yawa kafin sace shanu da yawa.
Harin ya tilastawa mazauna kauyen yin hijira zuwa babban birnin jihar, Maiduguri amma su kan dawo kauyen zuwa gonakinsu domin suyi aiki.
Boko Haram sun tsananta kai hari a garin Mammanti ne sakamakon zargin mazauna kauyen da kaiwa sojojin Najeriya bayyanan sirri a kansu.
Duk da cewa gwamnatin Najeriya ta cigaba da nanatawa cewar an ci galaba a kan Boko Haram, kungiyar ta kai hari a sansanin sojoji cikin kwana-kwanan nan a jihar Borno inda suka kashe sojoji da fararen hula.
Sama ta mutane 27,000 sun rasa rayyukansu sakamakon rikicin na Boko Haram tun shekarar 2009 kuma a kalla mutane 1.8 miliyan sun rasa muhallinsu a cewar AFP.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng