Zamfara ta sake rincabewa: An kashe jami'an tsaron sa kai 12, an kone babura

Zamfara ta sake rincabewa: An kashe jami'an tsaron sa kai 12, an kone babura

Wasu da ake kyautata zaton 'yan bindiga ne sun yiwa wasu jami'an sa kai na Civilian JTF 12 kwantar bauna a karamar hukuma Shinkafi na jihar Zamfara kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Mafi yawancin jami'an JTF din mazauna garin Kware ne da Kurya kuma suna kan hanyarsu na komawa gida ne daga wani taro da suka halarta a Shinkafi yayin da 'yan bindigan suka far musu inda suka kashe mutum 12.

Makonni biyu da suka gabata, gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da cewa za ta dauki sabbin jami'an JTF 8,500 a yunkurinta na kawo karshen yawan kashe-kashe da garkuwa da mutane a jihar.

Zamfara ta sake rincabewa: An kashe jami'an tsaron sa kai 12, an kone babura
Zamfara ta sake rincabewa: An kashe jami'an tsaron sa kai 12, an kone babura
Asali: Twitter

Mazauna garin sun shaidawa majiyar Legit.ng Hausa cewa jami'an Civilian JTF din suna tafiya ne a kan baburansu a cikin daji kwatsam sai yan bindigan suka far musu inda suka kashe su sannan suka kone baburansu.

DUBA WANNAN: An kashe mutane, an kona gidaje da mota a wani biki a jihar Bauchi

"Sun bude musu wuta inda suka kashe 12 cikinsu duk da cewa sunyi kokarin kare kansu amma 'yan bindigan sunfi karfinsu saboda irin bindigogin su na zamani ne yayin da JTF na amfani ne da bindigan masu farauta na gargajiya. A halin yanzu da na ke maka magana an gano gawarwaki 10 kuma bayan na bar wajen an gano wasu gawawakin biyu," inji Sani Kware.

Sai dai Kakakin 'yan sandan jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu ya ce an kira su misalin karfe 6.05 na yamma inda aka ce 'yan bindiga sun ritsa Civilian JTF na Kurya da Kware a hanyarsu ta komawa gida.

Ya ce nan take hukumar ta tura jami'anta na PMF, CTU da FSARS karkashin jagorancin DPO na Shinkafi domin su gano abinda ke faruwa.

"Mun samu gawa guda daya sannan an samu mutane biyu da raunukan bindiga inda aka garzaya da su zuwa asibitin garin Shinkafi domin yi musu magani"

"Kazalika, akwai babura da yawa a wajen wasu daga cikinsu an kone su. Jami'an mu sun fara bincike cikin dajin domin bin sahun yan bindigan ko kuma ceto wasu mutanen," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164