An sauya sunan ‘Dan takarar da yayi nasara a zaben fitar da gwani a Bakori/Danja

An sauya sunan ‘Dan takarar da yayi nasara a zaben fitar da gwani a Bakori/Danja

Mun ji cewa wanda ya lashe zaben fitar da gwani a Jam’iyyar APC mai mulki na ‘Dan Majalisar Tarayya na Yankin Bakori da ‘Danja watau Injiniya Yakubu Nuhu Danja ya koka da cewa APC ta sauya sunan sa.

An sauya sunan ‘Dan takarar da yayi nasara a zaben fitar da gwani a Bakori/Danja
Wanda ke neman kujerar Majalisa na Bakori da Danja ya kai kuka
Asali: Facebook

Injiniya Yakubu Nuhu Danja shi ne wanda ya lashe zaben tsaida ‘Dan takara da aka yi a Jam’iyyar APC inda ya samu kuri’a 314. Yakubu Nuhu Danja ya doke wanda ke kan kujerar ne watau Hon. Amiru Bakori a zaben da aka yi.

Malamin zaben Dr. Isah Adamu ya tabbatar da cewa Yakubu Nuhu Danja ne yayi nasara a takarar bayan Honarabul Amiru Bakori ya tashi da kuri’u 305. To sai dai kuma yanzu an ji cewa Jam’iyyar APC ta cire sunan Nuhu Danja.

Jam’iyyar APC mai mulki ta mikawa Hukumar zabe na kasa watau INEC sunan Amiru Bakori ne a matsayin ‘Dan takaran ta duk da cewa ba shi bane yayi nasara a zaben fitar da gwani da aka yi kwanaki inji Jaridar Daily Trust.

KU KARANTA: Mataimakin Gwamnan Jihar Sokoto Tambuwal ya yi murabus don dole

‘Dan takaran Jam’iyyar, Nuhu Danja ya nemi a cire sunan Abokin takaran na sa a maye gurbin da sunan sa amma hakan bai yiwu ba. Danja yace manyan APC a Katsina sun yi kokarin ganin an sa sunan sa amma abu ya ki yiwuwa.

Danja wanda ya sa ran zuwa Majalisar Tarayya yace sai da Mai Girma Gwamnan Katsina Aminu Bello Masari da kuma Shugaban APC na Jihar Shitu Shitu su kayi yunkurin a cire sunan Amiru Bakori amma APC ta yi kunnen-kashi.

Dazu kun ji Adams Oshiomhole yace APC ta kammala batun tsaida ‘Yan takara kuma har an mika sunayen masu takara a 2019 zuwa ga Hukumar zabe na kasa. Oshimhole yac sai dai APC ta ba 'Ya 'yan ta hakuri.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng