Kisan basarake a jihar Kaduna: Hukumar 'yan sanda ta kama mutane 93

Kisan basarake a jihar Kaduna: Hukumar 'yan sanda ta kama mutane 93

A yau Litinin, hukumar 'yan sandan Najeriya ta sanar da cewar ta kama wasu mutane 93 da ake zargi da hannu cikin kisar basaraken garin Adara a jihar Kaduna, Agwom Adara, Maiwada Rapheal Galadima.

An dai sace Galadima ne a ranar 19 ga watan Oktoban 2018 tare da matarsa wanda hakan ya haifar da barkewar rikici a Kasuwan Magani da wasu sassan jihar.

Daga bisani wanda su kayi garkuwa da basaraken sun kashe shi bayan sun karbi kudin fansa wanda hakan ya sa wata sabuwar rikicita sake barkewa a jihar.

Kisan basarake a jihar Kaduna: Hukumar 'yan sanda ta kama mutane 93
Kisan basarake a jihar Kaduna: Hukumar 'yan sanda ta kama mutane 93
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Karin bayani kan gawar Janar Alkali da aka kashe a Dura-Du a Jos

Kakakin hukumar 'yan sanda, DCP Jimoh Moshood ya shaidawa manema labarai a Abuja cewar hukumar ta kama wasu mutane da ake zargi da hannu cikin kisan basaraken amma bai bayyana sunayensu ba.

Ya yi bayyani cewar an yanke hukuncin ga 43 cikin wadanda aka kama yayinda sauran 50 suna tsare hannun yan sanda kuma ana cigaba da gudanar da bincike a kansu.

Ya bayyana cewar wadanda aka kama din sun hada da mabiyya addinai daban-daban a jihar ta Kaduna. Ya ce sufeta Janar na 'yan sanda ya bayar da umurnin a hukunta duk wanda aka samu da hannu cikin rikicin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164