Abin babba ne: El-Rufai ya koma ran gadin jihar Kaduna a jirgin sama (Hotuna)
A yunkurinsa na ganin an dawo da zaman lafiya a jihar Kaduna, Gwamna Mallam Nasir El-Rufai na cigaba da kaiwa da komowa tare da tattaunawa da Majalisar Tsaro na jihar domin ganin kurar ta lafa.
A kan wannan gabar ne gwamna El-Rufai tare da Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Ahmad Abdurahman suka shiga jirgi mai saukan ungulu suka zaga domin duba yadda al'ammura ke kasancewa karkashin dokar hana zirga-zirga na sa'o'i 24 da aka saka a jihar.

Asali: Twitter

Asali: Twitter
A baya, Legit.ng ta kawo muku cewar gwamnan ya ziyarci wasu unguwani a jihar a daren jiya domin duba yadda lamura ke tafiya tare da karin gwiwa ga jami'an tsaro da ke aikin kwantar da tarzomar.
Kazalika, gwamnatin na jihar Kaduna ta sanar da sassauta dokar hana zirga-zirgar a karamar hukumar Kachia bayan nazari kan yadda al'ummar garin ke biyaya da da'a da dokar da gwamnati ta saka.

Asali: Twitter
DUBA WANNAN: 2019: Yarabawa sunyi kaca-kaca da Fashola kan yiwa Buhari kamfe

Asali: Twitter
A dai karamar hukumar Kachia ne wasu 'yan bindiga da ba'a gano ko wanene ba suka sace basarake Agom Adare da matarsa inda daga baya suka sako matarsa amma shi suka kashe shi.
Gwamnatin jihar Kaduna ta mika ta'aziyyar ta ga iyalan basaraken da al'ummar garin na Kachia bisa rashin basaraken tare da yin alkawarin gudanar da bincike domin gano wadanda suka aikata mummunan aikin.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng