Abubuwan da Jafar Jafar ya bayyanawa Majalisar Kano a zaman da aka yi kan binciken Ganduje

Abubuwan da Jafar Jafar ya bayyanawa Majalisar Kano a zaman da aka yi kan binciken Ganduje

Mawallafin gidan Jaridar nan ta Daily Nigerian, Malam Jaafar Jaafar ya bayyana a gaban Majalisar dokokin Kano a jiya Laraba inda ya ‘Yan Majalisar Jihar su ka masa tambayoyi a binciken da ake cigaba da yi game da Gwamna Abdullahi Ganduje.

Abubuwan da Jafar Jafar ya bayyanawa Majalisar Kano a zaman da aka yi kan binciken Ganduje
Malam Jafar Jafar a gaban Majalisar dokokin Jihar Kano yana jawabi
Asali: Depositphotos

Mawallafin gidan Jaridar ya saki bidiyoyi inda aka ga Gwaamna Dr Abdullahi Umar Ganduje yana karbar makudan Dalolin da ake zargin cewa cin hanci ne daga hannun wasu ‘Yan kwangila. Hakan ta sa aka nemi yayi wa Majalisar Kano karin bayani.

Wata Jaridar kasar nan ta bayyana duk abin da ya wakana a Majalisar tun daga farko har karshe:

Jafar Jafar yace

1. Fiye da shekaru biyu kenan wani Aboki na da yake aikin kwangila yayi mani kukan cewa Mai Girma Gwamnan Kano na karbar na-goro har kashi 25% (na abin da aka kashe) idan har an yi wani aiki a Jihar Kano.

2. A dalilin haka ne mu kayi amfani da na’urar daukar hoto ta asiri mu ka samu hujjar kama Gwamna dumu-dumu. Dagan cikin bidiyoyi 15 da mu ka dauka, akwai akalla 9 da ke dauke da fuskar Mai Girma Gwamna yana karbar Daloli.

KU KARANTA: Mawallafin Daily Nigerian Jafar Jafar zai hallara gaban ‘Yan Majalisa

3. Kafin DAILY NIGERIAN ta buga wadannan labarai, sai da mu ka tabbatar da cewa bidiyoyin sahihai ne inda mu ka mikawa Ma’aikatan mu da kuma wadanda su ka san harkar bidiyo.

4. Haka kuma mun ba Kungiyar nan ta Amnesty International Nigeria, da Gidan BBC da kuma Jaridar PREMIUM TIMES wadanda duk su ka tabbatar mana cewa bidiyon ba dabo bane kafin mu saki a Duniya.

5. A Ranar 14 ga Watan Oktoba mu ka fara sakin wannan bidiyo inda aka ga Gwamna kuru-kuru yana karbar Dalolin Amurka yana cusawa a cikin babbar rigar sa da kuma wata ambula har a wurare 2.

6. A shirya nake in ba ku wannan bidiyoyi a yadda su ke ku gani da idanun ku domin ku yi binciken ku a Majalisa.

7. Nagode da wannan kwamiti su ka bani dama na bayyana a gaban ta domin in yi karin haske game da wannan lamari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng