Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta bayyana matsayar ta kan batun karin albashi

Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta bayyana matsayar ta kan batun karin albashi

Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta bayyana cewar ba ta adawa ta yiwa ma'aikata karin mafi karancin albashi da Kungiyar Kwadago na kasa ke nema.

Ciyaman din kungiyar, Gwamna Abdulaziz Yari na jihar Zamfara ne ya bayyana wa manema labarai hakan a jiya Laraba bayan kungiyar tayi taro a Abuja.

Ya ce matsalar ba wai adadin mafi karancin albashin da gwamnonin za su iya biya bane amma samuwar kudaden da gwamnonin za suyi amfani dashi domin biyan albashin da kungiyar kwadago (NLC) ke bukata.

Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta bayyana matsayar ta kan karin albashi
Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta bayyana matsayar ta kan karin albashi
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Karyar rage shekaru: Gwamna PDP ya shiga tsaka mai wuya

Yari ya ce a halin yanzu akawai jihohi da dama da basu iya biyan N18,000 din yayinda wasu jihohin ke biyan 35% wasu kuma suke biyan 50% kana wasu jihohin ma akwai bashi a kansu.

"Matsalar ba karin albashin bane amma inda za mu nemo kudaden da zamu biya sabon albashinm," inji Yari.

Kazalika, Yari ya bayyana cewar kungiyar ta gayyaci shugaban NLC, Comrade Ayuba Wabba domin ya yiwa kungiyar bayani kan yadda jihohi su kayi amfani da kudin London da Paris Club da gwamnatin tarayya ta basu.

Gwamnatin Tarayyar ta bayar da kudaden ne da yarjejeniyar cewar za suyi amfani da kasho mai tsoka na kudin domin biyan albashin ma'aikata.

Ya kuma ce sun saka hannu yarjejeniyar fahimtar juna da NLC kan yadda za a magance matsalar biyan albashin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel