Takarar gwamna: PDP ta tsayar da Takai a Kano, ta yi watsi da surukin Kwankwaso

Takarar gwamna: PDP ta tsayar da Takai a Kano, ta yi watsi da surukin Kwankwaso

Uwar jam’iyyar PDP ta yi watsi da dan takararta na mukamin gwamnan jahar Kano, kuma surukin jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Abba K Yusuf, inda ta tabbatar da Salihu Sagir Takai a matsayin sabon dan takararta a zaben 2019.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito uwar jam’iyyar ta dauki wannan mataki ne a ranar Alhamis, 11 ga watan Oktoba biyo bayan nuna rashin amincewa da sauran yan takarar gwamna a jam’iyyar suka nuna game da yadda aka gudanar da zaben fidda gwani a gidan Kwankwaso.

KU KARANTA: Sabon gwamna sabon sarki: APC ta yi juyin mulki a majalisar dokokin jahar Ekiti

Haka zalika majiyar Legit.ng ta ruwaito Takai ya samu goyon bayan shuwagabannin jam’iyyar PDP na kananan hukumomin talatin da takwas daga cikin arba’in da hudu da ake dasu a jahar Kano a wani kwarya kwaryan taro da aka yi a Abuja.

Takarar gwamna: PDP ta tsayar da Takai a Kano, ta yi watsi da surukin Kwankwaso
Takai da Abba
Asali: UGC

Sai dai har zuwa lokacin tattara wannan rahoto, majiyarmu ba ta samu Kaakakin jam’iyyar PDP Kola Ologbondiyan ba, don ta jin ta bakinsa, sakamakon lambobin wayoyinsa duka ba sa shiga.

Sai dai wani dan gani kashenin Kwankwasiyya, kuma aminin tsohon gwamnan jahar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Mohammad Digol ya bayyana matakin da PDP ta dauka a matsayin karya doka, inda yace lokacin shirya zaben fidda gwani ya wuce, kuma duk wani taron jam’iyya da aka yi a wajen Kano haramtacce ne.

Idan za’a tuna Yusuf K Abba ya zama dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP ne a ranar 2 ga watan Oktoba a wani zaben fidda gwani dake cike da cecekuce daya gudana a gidan surukinsa, Kwankwaso dake Lugar Avenue.

Da fari, jam’iyyar ta yi nufin shirya zaben nata a Marhaba silima, sai dai jami’an Yansandan jahar Kano sun garkame siliman, inda suka ce suna amfani da umarnin Kotu ne da ta hana duk wani tsagin jam’iyyar PDP shirya taro, sakamakon karar da shugaban tsagin PDP, Doguwa ya shigar gabanta.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel