El-Rufa'i ya ziyarci Sheikh Algarkawee da 'yan bindiga suka sace kwanakin baya

El-Rufa'i ya ziyarci Sheikh Algarkawee da 'yan bindiga suka sace kwanakin baya

A yau, Laraba, ne gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i ya ziyarci babban malamin addinin Islama, Sheikh Adam Algarkawee, da 'yan bindiga suka sace kwanakin baya tare da wasu almajiransa.

An saki makamin ne bayan biyan kudin fansa, miliyan N10m, kamar yadda majiyar mu ta tabbatar. A ranar Alhamis ne wasu yan bindiga da suka yi awon gaba da fitaccen Malamin addinin Musunluncin nan dake zaune a jihar Kaduna, Sheikh Ahmad Al-Garkawy tare da wasu dalibansa.

El-Rufa'i ya ziyarci Sheikh Algarkawee da 'yan bindiga suka sace kwanakin baya
El-Rufa'i ya ziyarci Sheikh Algarkawee

Jaridar Desert Herald ce ta ruwaito wannan labari, inda tace yan bindigan sun yi garkuwa da shehin Malamin tare da dalibansa ne a ranar Alhamis, 2 ga watan Agusta, a daidai lokacin da suka kai ziyara gonar makarantarsa dake gefen garin Kaduna.

DUBA WANNAN: Fadar shugaban kasa tayi karin haske a kan rahoton karin wa'adin hutun Buhari

Duk da irin kokarin da gwamnatin tarayya take yi game da yaki da masu garkuwa da mutane a Najeriya, amma ayyukansu na cigaba da ta’azzara a yankin Arewa maso yamma, musamman ma a jihar Kaduna, lamarin da yafi shafar al’ummar garin Birnin Gwari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel