Tsige Saraki: An bawa Sanatocin APC miliyan $1m

Tsige Saraki: An bawa Sanatocin APC miliyan $1m

Sanata Rafi’u Ibrahim, mai wakiltar jihar Kwara ta kudu ya zargi ‘yan majalisar dattijai na jam’iyyar APC da karbar cin hancin dalar Amurka miliyan $1m domin tsige shugaban majalisar, Bukola Saraki da mataimakinsa, Ike Ekweremadu.

Dan majalisar ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai a harabar majalisar dattijai a yau, Talata.

Mista Ibrahim, daya daga cikin masu goyon bayan Bukola Saraki, ya yi alla-wadai da kutsen da jami’an tsaro na DSS suka yiwa zauren majalisar a safiyar yau.

Zan iya tabbatar maku da cewar sanatocin dake yunkurin tsige Saraki sun karbi cin hancin dala miliyan $1m domin kawar da shi da mataimakinsa. Zan iya kare kai na a ko ina,” a cewar Mista Ibrahim.

Tsige Saraki: An bawa Sanatocin APC miliyan $1m
Bukola Saraki

Da safiyar yau ne jami’an hukumar DSS sun mamaye majalisar dokokin kasar a yayinda ake yunkurin sake bude zangon majalisar ga yan majalisa masu biyayya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari.

DUBA WANNAN: A kan sharadi daya ne kawai zamu janye hutun da muka tafi - 'Yan majalisa

Babban sakataren labarai na majalisar dattawa, Sanni Onogu ya tura sako ga manema labarai dake daukar rahoton majalisar dokokin kasar a daren jiya kan cewa su zama a shirye domin ana iya bude majalisar a yau. Sai dai wasu yan jarida da suka isa zangon a safiyar yau Talata, 7 ga watan Agusta basu samu shiga ba sakamakon mamaye zangon da jami’an DSS suka yi.

Haka kuma an hana jami’an shiga zangon. Babuwani bayani da aka ba manema labarai wadda suka tursasa don son sanin dalilin hana su shiga zangon.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng