Yadda wasu matsaloli suka kusa raraka ta daga kan mulki – Gwamna Abubakar

Yadda wasu matsaloli suka kusa raraka ta daga kan mulki – Gwamna Abubakar

Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Abubakar Badaru, ya yi waiwaye a kan yadda wasu matsaloli da ya gada daga gwamnatin da ta gabace shi suka kusa saka shi barin kujerar sat a gwamna bayan an rantsar das hi a shekarar 2015.

Da yake bayyana matsalolin da ya fuskanta ga manema labarai a gidan gwamnatin jihar Dutse a jiya, Litinin, Badaru, ya ce tulin takardun bashi da aiyukan da ba a karasa ba da suka kai biliyan N31.3 ne suka saka shi fara tunanin barin kujerar gwamnan jihar Jigawa da aka zabe shi.

Gwamnan ya kara da cewar matakan matse bakin aljihu da tsantseni day a dauka ne suka bashi dammar cigaba da zama a kujerar sa duk da daukan matakin ya jawo masa bakin jinni wurin jama’a da dama, har daga cikin jam’iyyar APC.

Yadda wasu matsaloli suka kusa raraka ta daga kan mulki – Gwamna Abubakar
Gwamna Badaru Abubakar

Badaru ya cewar, gwamnatin sat a kasha biliyan N51bn a ginin hanyoyi a fadin jihar Jigawa, aiyukan da yace sun hada da na biliyan N31.3bn day a ce ya gada daga hannun waccan gwamnati da kuma sabbin hanyoyi day a kirkira na biliyan N19.3bn.

DUBA WANNAN: Tinubu ya fara zawarcin wasu fitattun 'yan Najeriya biyu zuwa APC

Sannan ya kara da cewar, “gwamnatin PDP da na gada ta bar miliyan N16m cikin asusun jihar don kada ko kudin biyan albashi mu samu amma bayan mun dauki matakan matse bakin aljihu da tsantseni, sai gas hi yanzu jihar mu na daga cikin jihohin Najeriya dake iya biyan ma’aikata albashi a kan lokaci.”

Gwamnan yace yana gaba-gaba a cikin gwamnonin Najeriya da suka bawa bangaren noma fifiko da muhimmanci .

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng