Gaba da gaban ta: ‘Yan fashin da suka tare hanyar Buratai a Adamawa sun ji maza, kalli hotunan su
A daya daga cikin labaran Legit.ng na yau, kun ji cewar wasu ‘yan fashi da suka tare hanyar Numan zuwa Yola a jihar Adamawa sun gamu da fushin dakarun sojin tawagar shugaban sojojin kasa, Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun darektan hukumar sojin, Birgediya Texas Chukwu, ta bayyana cewar a jiya Asabar, 5 ga watan Mayu, tawagar shugaban sojin kasa ta kama wasu ‘yan fashi da suka tare hanya suke zaluntar mutane kuma Buratai ya biyo hanya. ‘Yan fashin sun tare babbar hanyar inda suke cin Karen su ba babbaka kafin tawagar Buratai ta zo wuce wa ta hanyar.
An kama wasu makamai a hannun ‘yan fashin da suka hada da; bindigar baushe guda uku, adduna, da wasu tarkacen tsibbu.
Sanarwar ta bayyana cewar tuni dakarun sojin suka mika ‘yan fashin hannun jami’an ‘yan sanda domin zurfafa bincike da gurfanar das u gaban shari’a.
Hukumar soji ta bukaci jama’a da suke samar da bayanai masu muhimmanci ga jami’an tsaro a kan kari domin daukan mataki kafin lamari ya rincabe.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng