A karo na farko, za'a gina wa Kiristoci coci a kasar Saudiyya

A karo na farko, za'a gina wa Kiristoci coci a kasar Saudiyya

- Babban daulan musulunci na kasar Saudiyya ta amince cewa zata gina wa Kiritoci mazuna kasar coci

- Kasar ta Saudiyya ta ratabba hannu kan wata yarjejeniya da shugaban cibiyyar harkokin addinai mabanbanta na duniya

- Wasu masu sharhi sun ce haba-haban da kasar ta Saudiyya keyi ga sauran wadanda ba musulmi ba yana da nasaba na kokarin rage dogaro a kan man fetur a matsayin jagaban tattalin arzikin kasar

Mun samu rahoton cewa kasar Saudiyya ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da kasar Vatican inda zata fara coci-coci saboda mabiyya addinin Kirista da ke zaune a kasar ta Saudiyya kamar yadda Breitbart ta wallafa.

Rahotton yace babban sakataren kungiyar kasashen musulmi 'Muslim World League', Sheikh Mohammed bin Abdel Karim Al-Issa ne ya sanya hannu kan yarjejeniyar tare da shugaban 'Pontifical Council for Inter-religious Dialogue' na kasar Vatican, Cardinal Jean-Louis Tauran.

A karo na farko, za'a gina wa Kiristoci coci a kasar Saudiyya
A karo na farko, za'a gina wa Kiristoci coci a kasar Saudiyya

KU KARANTA: Kungiyar musulmi ta JNI ta bukaci jama'a su farga saboda jami'an tsaro sunyi sanyi

Kafan yadda labaran na Breitbert kuma ta ruwaito cewa maraba da kasar ta Saudiyya keyi da al'adu da addinan sauran mutanen duniya na da nasaba da kokarin rage dogara a kan man fetur a matsayin jagaban tattalin arzikin kasar.

A yarjejeniyar da kasashen biyu saka rattaba hannu a kai, kasashen biyu zasu kafa wata kwamitin hadin gwiwa mai wakilai biyu daga bagarorin biyu domin su cigaba da tsara yadda za'a cinma nasarar aikin.

An kuma ruwaito cewa kwamitin za ta rika gudanar da taron ta ne sau daya a kowanne mako inda za'a rika yin taron a birnin Rome da kuma ko wane gari da kasar Saudiyya ta zaba.

Kawo yanzu, kasar Saudiyya ce kawai kasar larabawa da ba ta da coci ko guda kamar yadda rahoton ya bayyana. Hakan yana da nasaba da akidar Wahabiyyanci da kasar ke kai wanda ya haramta gudanar da wasu addinan da ba musulunci ba.

Wata jaridar kasar Vatican ta ruwaito cewa, Tauran ya ce yana matukar farin ciki da wannan sabon shafi da kasar ke budewa. "Alama ce da ke nuna cewa mahukuntan kasar Saudiyya suna da niyyar kawo canji a kasar," inji shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel