Duk kudin sa: Dubi Budurwar da ke yi wa Dan wasa Ronaldo wulakanci

Duk kudin sa: Dubi Budurwar da ke yi wa Dan wasa Ronaldo wulakanci

– Babban dan wasan Duniya Cristiano Ronaldo ya nemi wata budurwa ta nuna ba ta son sa

– Duk kudin dan wasan Tauraruwa Lilia ta ga bai burge ta ba

– Abin dai ya faskara ga dan wasan da ya fi kowa a Duniya

Duk kudin sa: Dubi Budurwar da ke yi wa Dan wasa Ronaldo wulakanci
Duk kudin sa: Dubi Budurwar da ke yi wa Dan wasa Ronaldo wulakanci

Dan wasan Duniya Cristiano Ronaldo wanda shi ne zakaran duniya na bana ya nemi wata budurwa amma abu ya faskara. Mun samu labari daga Jaridun kasar Spain cewa dan wasan ya nemi wata budurwa amma da alamu ta yi watsi da shi.

Ronaldo wanda yayi fice a Duniya yana neman wata Tauraruwar kasar Rasha Lilia Ermak amma ta ki ba sa dama su hadu. Lilia Ermak dai tana zama ne a Birnin Miami kuma tayi fice a Duniya wajen harkar gayu.

KU KARANTA: Shugaban Amurka ya kira shugaban kasar Najeriya

Duk kudin sa: Dubi Budurwar da ke yi wa Dan wasa Ronaldo wulakanci
Duk kudin sa: Dubi Budurwar da ke yi wa Dan wasa Ronaldo wulakanci

Ronaldo wanda yake da d’a guda daya ya taba soyayya da wata ‘yar kasar Rashar mai suna Irina Shaykh daga baya kuma suka rabu. Watakila dai ita Lilia ba ruwan ta da ‘yan wasan kwallon kafa ne. Yanzu haka dai Ronaldo na tare da wata wai ita Georgina Rodriguez.

A Ingila kuma wasu tsageru sun kai hari gidan wani dan wasan Liverpool saboda jin haushin ya zubar da finariti a Gasar cin kofin nahiyar Afrika. Dan wasa Mane ya barar da bugun daga kai sai mai tsaron gida a Gasar AFCON, wasu suka ce da gan-gan yayi hakan.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel