Da Duminsa: Gusau ya Lashe Zaben Kujerar Shugabancin NFF

Da Duminsa: Gusau ya Lashe Zaben Kujerar Shugabancin NFF

  • Alhaji Ibrahim Musa Gusau ya zama sabon shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya, NFF a zaben da aka yi a yau
  • Ya lallasa 'yan takara 9 inda ya zama sabon shugaban da aka zaba a birnin Benin dake jihar Edo a zaben yau Juma'a
  • Ya samu kuri'u 22 inda ya lallasa Akinwumi mai kuri'u 12 da kuma Garba dake biye da shi mai kuri'u 6

Edo - Alhaji Ibrahim Musa Gusau ya tabbata sabon zababben shugaban Hukumar Kwallon kafa ta Najeriya, NFF.

An zabe shi sabon shugaban NFF a zabensu karo na 78 a birnin Benin dake jihar Edo a ranar Juma'a, The Nation ta rahoto hakan.

Ibrahim Gusau NFF
Da Duminsa: Gusau ya Lashe Zaben Kujerar Shugabancin NFF. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: UGC

Gusau ya samu kuri'u 21 inda ya lallasa mai biye da a bayana Barista Seyi Akinwumi wanda ya samu kuri'u 12 yayin da Shehu Dikko ke biye da kuri'u shida.

Kara karanta wannan

Jerin Sunayen 'Yan Takara 10 na Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya

Duk da Gusau bai samu kuri'u 22 da ake bukata ba ta zama shugaban NFF, sauran masu neman kujerar sun sha kaye.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Karin bayani na nan tafe...

Jerin Sunayen 'Yan Takara 10 na Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya

A wani labari na daban, hukumar kwallon kafa ta Najeriya, NFF, za ta zabi sabon shugaba na 40 a gagarumin taronta na shekara-shekara da take yi karo na 78 a babban birnin Benin dake jihar Edo a ranar Juma'a.

Duk wanda yayi nasarar zama sabon shugaban NFF, zai kasance shugaban hukumar na 36 tun bayan lokacin da aka kafa kungiyar a 1945.

Mutum goma ne ke takarar maye gurbin shugaban hukumar NFF mai barin gado, Amaju Pinnick

Asali: Legit.ng

Online view pixel