Jerin Sunayen 'Yan Takara 10 na Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya

Jerin Sunayen 'Yan Takara 10 na Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya

Edo - Hukumar kwallon kafa ta Najeriya, NFF, za ta zabi sabon shugaba na 40 a gagarumin taronta na shekara-shekara da take yi karo na 78 a babban birnin Benin dake jihar Edo a ranar Juma'a.

Duk wanda yayi nasarar zama sabon shugaban NFF, zai kasance shugaban hukumar na 36 tun bayan lokacin da aka kafa kungiyar a 1945.

Amaju Pinnick
Jerin Sunayen 'Yan Takara 10 na Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

Mutum goma ne ke takarar maye gurbin shugaban hukumar NFF mai barin gado, Amaju Pinnick

Ga jerin sunayen 'yan takaran goma:

Peterside Idah

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idah tsohon gola Suoer Eagles ne wanda yayi wasanni masu tarin yawa a gida Najeriya. Idah yana da shekaru 47 kuma fasto ne mai kula da Christ Ambassadors Church a Johannesburg, South Africa.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: An fara kamfen zaben 2023, jigon APC ya ce bai san inda Tinubu yake ba

Christian Emeruwa

Emeruwa yana da digirin-digirgir a fannin Health Education and Human Kinetics daga jami'ar Ibadan kuma ya shugabanci CAF a fannin tsaro a Cairo.

David Doherty

Doherty sabon suna ne ga dukkan masu lura da lamurran kwallon kafa a Najeriya. Tsohon 'dan wasn kwallon kafa ne, Yayi wa Concord FC da Water Corporatin wasa kafin ya dena kwallo saboda raunin da ya samu a kafa.

Ibrahim Gusau

Gusai mamba ne a kwamitin CAF kuma shugaban FA na jihar Zamfara.

Seyi Akinwunmi

Akinwumi lauya ne wanda ya taba aiki a kwamitin wucin-gadi na tsarin sake Nigeria National League a 2012.

Shi ne mataimakin shugaban NFF na farko. Akinwumi ya fara shiga ofis ne a 2014 kuma an sake zabensa a 2018.

Shehu Dikko

Dikko haifaffen Kaduna ne kuma shi ne shugaban League Management Company ( LMC).c

Abba Yola

Yola shugaban ma'aiktan ministan wasannin ne, Sunda Dare kuma yana neman kujerar NFF a karo na biyu bayana Amaju Pinnick ya lallasa shi a 2018.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Hotuna Sun Bayyana A Yayin Da Peter Obi Ya Kaddamar Da Kamfen Dinsa A Babban Jihar Arewa

Adam Mohammed

Mohammed shugaban FA ne dake hangen kujerar NFF. Kwararre ne a harkar kudi na shekaru da dama.

Suleiman Kwande

Suleiman Kwande tsohon 'dan majalisa ne daga jihar Filato wanda ke hango hayewa kujerar shugabancin NFF. Bayan ga zama 'dan siyasa, Kwande mamba ne mai wakiltar arewa ta tsakiya a NFF.

Musa Amadu

Musa Amadu tsohon sakatare janar na NFF ne a yayin mulkin Aminu Maigari kuma yana fatan yin caraf da kujerar shugabancin daga Pinnick a zaben da za a yi ranar 30 ga watan Satumba.

Fitaccen Dan Wasan Najeriya, Ahmed Musa, Ya Kwanta Asibiti, An Masa Tiyata

A wani labari na daban, Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles, Ahmed Musa, ya kwanta a asibiti inda likitoci suka yi masa tiyata.

Jarumin kwallon kafan ya je shafinsa na Instagram a ranar Laraba, 28 ga watan Satumba domin godiya ga Allah kan nasarar da aka samu wajen yi masa aikin a hannunsa na hagu.

Kara karanta wannan

Babu Banbanci Tsakanin Obi, Atiku Da Tinubu, In Ji Kachikwu, Dan Takarar Shugaban Kasa Na ADC

Musa ya mika godiyarsa ga hazikan likitocin da aka sanya su yi masa aikin kan namijin kokarin da suka yi wajen inganta masa lafiyar jikinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel