Bayan shekaru kusan 30, Buhari ya tuna da Super Eagles, ya cika alkawarin da aka yi masu

Bayan shekaru kusan 30, Buhari ya tuna da Super Eagles, ya cika alkawarin da aka yi masu

  • Gwamnatin Tarayya ta yarda a raba gidaje ga ‘yan wasan Super Eagles da suka yi kwallo a 1994
  • Shugaba Muhammadu Buhari ya tuno da tsohon alkwarin da aka yi wa taurarin a shekarun baya
  • An bayyana wannan ne yayin da ake bikin bude wasu gidaje da gwamnati ta gina a jihar Nasarawa

Abuja - Gwamnatin tarayya ta amince da rabon gidaje ga tsofaffin ‘yan wasan kwallon kafa da suka bugawa kasar Najeriya shekaru 28 da suka wuce.

Premium Times ta ce shugaba Muhammadu Buhari ya dauki nauyin cika alkawarin da aka yi wa wadannan ‘yan kwallon kafa 22 a tun a wancan lokacin.

Wani jawabi daga ma’aikatar ayyuka da gidaje na kasa ya tabbatar da cewa Mai girma shugaban kasa ya amince a raba gidajen ga tsofaffin taurarin kasar.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Tsohon dan wasan kwallon Najeriya ya yanki jiki ya fadi matacce a Jos

Janar Sani Abacha ne yake mulki a lokacin da aka yi wa ‘yan wasan kwallon kafan wannan alkawari. Sojan ya rasu kafin ya cika alkawarin a 1998.

An gina gidaje a Lafia

An bayyana wannan ne a a wajen bikin bude gidajen da gwamnati ta gina a Lafia, jihar Nasarawa. Nan gaba za a kammala gidajen da aka gina a jihohi 34.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Karamin Ministan kimiyya da fasaha da kirkire-kirkiren zamani, Muhammed Abdullahi ya wakilci Muhammadu Buhari wajen bude wannan gidaje.

Super Eagles
Super Eagles a USA 1994 Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Darektan gidaje da gine-gine na ma’aikatar tarayya, Solomon Labafilo ya bayyana cewa an kammala ginin gidaje 76 masu daki daya zuwa uku a Lafia.

Su wanene 'yan tawagar Super Eagles 94?

Kamar yadda bayanai su ka nuna a shafin FIFA, ‘yan wasan Najeriya da suka buga gasar cin kofin Duniya a 1994 sun hada da Peter Rufai mai tsaron gida.

Kara karanta wannan

Kafin Ramadan zamu maida Magidanta 500 da tallafin N100,000 ga kowa Insha Allahu, Zulum

Akwai Augustine Eguavoen, Ben Iroha, Stephen Keshi, Uche Okechukwu, Chidi Nwanu, Finidi George, Thompson Oliha, Rashid Yakini da J. J Okocha.

Sauran su ne Emmanuel Amunike, Samson Siasia, Daniel Amokachi, Sunday Oliseh, Mutiu Adepoju, Victor Ikpeba, Micheal Emanolo da sauransu.

Stephen Keshi ne ya jagoranci ‘yan wasan suka lashe gasar AFCON 1994. Bayan kusan shekaru 10, suka sake daukar kofin yayin da Marigayi Keshi ya ke koci.

Ina batun sabon koci?

Kwanaki baya rahoto ya zo maku cewa hukumar kwallon kafar NFF ta fasa daukar hayar Jose Peseiro a matsayin sabon kocin 'yan wasan Super Eagles.

Sakataren NFF na kasa, Mohammed Sanusi ya bayyana cewa ba su da bukatar yin aiki da Peseiro. Augustine Eguavoen zai cigaba da horas da 'yan kwallon.

Asali: Legit.ng

Online view pixel