Najeriya tayi watsi da Baturen koci, ta fadi wadanda za su horas da 'Yan Super Eagles

Najeriya tayi watsi da Baturen koci, ta fadi wadanda za su horas da 'Yan Super Eagles

  • Hukumar kwallon kafar NFF ta fasa daukar hayar Jose Peseiro a matsayin sabon kocin Najeriya
  • Sakataren NFF na kasa, Mohammed Sanusi ya bayyana cewa ba su da bukatar yin aiki da Peseiro
  • Augustine Eguavoen zai rike kujerar kocin Super Eagles tare da taimakon Emmanuel Amuneke da Yusuf

Abuja - Hukumar kwallon kafa ta Najeriya ta bada sanarwar cigaba da aiki da Austin Eguavoen a matsayin kocin tawagar Super Eagles na rikon kwarya.

Jaridar The Cable ta ce NFF ta bada wannan sanarwa ne a ranar Litinin, 7 ga watan Fubrairu 2022.

Hukumar ta NFF ta ce tayi watsi da maganar nada Jose Peseiro a matsayin sabon kocin ‘yan wasan kwallon kafa na Najeriya bayan kammala gasar AFCON.

Kara karanta wannan

Mun shiga uku: Tsadar man fetur ya sa 'yan Najeriya kuka, sunyi zazzafan martani

Sakataren NFF na kasa, Mohammed Sanusi ya ce yanzu ba a bukatar aikin Peseiro a sakamakon shawarar da kwamitinsu ya bada cewa a rike kocin rikon kwaryan.

Mohammed Sanusi ya godewa Peseiro, ya ce su na fatan wata rana za su yi aiki tare da shi.

Emmanuel Amunike zai yi aiki da NFF

Tsohon ‘dan wasan tsakiyar Super Eagles, Emmanuel Amunike shi ne zai zama babban mataimakin koci. Shi da Salisu Yusuf za su taimakawa Eguavoen.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Super Eagles
Kocin Super Eagles Eguavoen Hoto: sportsbrief.com
Asali: UGC

Baya ga haka, Punch ta ce hukumar kwallon ta amince da wasu garambawul da aka yi wa tawagar masu horas da ‘yan wasan kwallon kafan na Najeriya.

Tsohon ‘dan wasan na kungiyar Barcelona, Amuneke ne ya jagoranci kasar Tanzaniya har ta samu zuwa gasar kofin nahiyar Afrika da aka yi a shekarar 2019.

Sauran ‘yan tawagar sun hada da tsohon ‘dan wasan bayan Najeriya, Joseph Yobo. Aloysius Agu ne aka zaba a matsayin babban mai horas da masu tsaron raga.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: APC ta tabbatar da ranar gudanar da babban taronta na kasa, 26 ga watan Fabrairu

Tawagar masu horaswa

Augustine Eguavoen – Darektan wasanni/Mai bada shawara (na rikon kwarya)

Emmanuel Amuneke – Babban koci/Mai taimakawa koci na farko

Salisu Yusuf – Mataimakin koci na biyu/Babban kocin CHAN

Joseph Yobo – Mataimakin koci na uku

Aloysius Agu – Mai horas da masu tsaron gida

Hakan na nufin Augustine Eguavoen zai jagoranci Najeriya a muhimmin wasan zuwa gasar cin kofin Duniya na 2022 da za ta buga da kasar Ghana a watan Maris.

Jose Peseiro: Ta leko, ta koma

A kwanakin baya an ji cewa Hukumar kwallon kafan na Najeriya ta nada Jose Peseiro a matsayin sabon kocin Super Eagles da nufin zai fara aiki bayan AFCON.

Kocin ya yi aiki a Afrika da wasu manyan kungiyoyin kwallon kafa da ake ji da su a Duniya. Peseiro ya na cikin mataimakan Carlos Queiroz da yake Real Madrid.

Kara karanta wannan

Jami'an Kwastam sun yi ram da manyan motoci 17 maƙare da buhunan Shinkafar kasar waje

Asali: Legit.ng

Online view pixel