Tsohon ‘Dan wasan Milan, Madrid ya bar Kiristanci, ya shiga Musulunci a dalilin matarsa

Tsohon ‘Dan wasan Milan, Madrid ya bar Kiristanci, ya shiga Musulunci a dalilin matarsa

  • A ranar Juma’a, 4 ga watan Maris 2022, Clarence Seedorf ya bada sanarwar cewa ya karbi musulunci
  • Tsohon ‘dan wasan ya shiga addinin musulunci ne a sanadiyyar mai dakinsa, Sophia Makramati
  • Seedorf wanda ya buga kwallo a Milan da Madrid ya ci gasar cin kofin nahiyar Turai da kungiyoyi 3

Nederlands - Clarence Seedorf wanda ya bugawa manyan kungiyoyin kwallon kafan Turai irinsu Real Madrid, Inter, AC Milan da Ajax ya canza addininsa a yau.

Rahotanni da suka fito daga Gulf News sun bayyana cewa a ranar Juma’ar nan ne tsohon ‘dan kwallon ya bada sanarwar cewa ya karbi addinin musulunci.

Clarence Seedorf ya yi magana a shafin yanar gizo, ya tabbatar da shigarsa addinin musuluncin.

Kara karanta wannan

Dirama a Kotu: Saurayin da ake zargi da kashe budurwarsa ya koma mawaƙi da ya ga shaidu

“Nagode da duka sakonni masu dadi da aka aiko mani, ana taya ni murnar shiga cikin ‘yanuwa musulmai.”
“Ina mai cike da farin cikin shiga cikin ‘yanuwana mata da maza musulmai da ke fadin Duniyar nan.”
“Musamman Sophia wanda ta sanar da ni game da hakikanin ma’anar musulunci. Ban canza sunana ba.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tsohon ‘Dan wasan Milan
Clarence Seedorf a Madrid Hoto: www.dailysabah.com
Asali: UGC

Seedorf ya canza suna?

Sahibarsa, Sophia Makramati ta tabbatar da haka a Instagram, amma kocin ya ce bai canza suna ba.

“Zan cigaba da amfani da sunan da iyaye na suka bani. Clarence Seedorf! Ina mai aika soyayya ga kowa a Duniya."

- Clarence Seedorf!

Jaridar nan ta Middles East Eye ta ce tun da Clarence Seedorf ya fito ya yi wannan bayani dazu, mutane daga ko ina a fadin Duniya suke ta tofa albarkacin bakinsu.

Tashi a addinin kirista

Kara karanta wannan

An gano sabon salon da Boko Haram suka dauka tun da dakarun Sojoji sun ci karfinsu

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa an haifi Clarence Seedorf ne a wani kauye da ake kira Paramaribo, garin Suriname a kasar Neverlands cikin addinin kiristanci a 1976.

Mahaifinsa Johann Seedorf da ‘yanwunsa Jürgen da Chedric Seedorf duk sun yi kwallon kafa. Tsohon ‘dan wasan tsakiyan ya yi shahada ne yana da shekara 45.

An yi wa Neymar sata

Kwanakin baya ku ka ji cewa 'Yan Sandan kasar Brazil sun cafke wani mutumi da ake zargin ya shiga asusun mutane ya sace masu kudi ba tare da sun ankara ba.

Wani ma’aikacin banki ne ake tuhuma da laifin sace Dala 40, 000 daga akawun din ‘Dan wasa Neymar. Tauraron bai san an dauki wannan kudi daga asusunsa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel