An samu ci gaba a Najeriya: Super Eagles sun haura matsayi na uku a nahiyar Afirka

An samu ci gaba a Najeriya: Super Eagles sun haura matsayi na uku a nahiyar Afirka

  • Najeriya ta sake haurawa matsayi mai girma a jerin kasashen duniya mafi matsayi inji rahoton kwallon kafa na FIFA
  • FIFA ta fitar da rahoton jerin kasashe mafi matsayi a kungiyyin kwallo, inda wasu suka sauka wasu kuma suka haura
  • Za a sake buga sabon rahoto irin wannan a karshen watan Maris, inda za a sake bayyana matsayin kowace kasa

Duk da ficewar Super Eagles ta Najeriya daga gasar cin kofin nahiyar Afirka da aka kammala a Kamaru da wuri, kungiyar ta haura matsayi uku a kididdigar da hukumar kwallon kafa ta duniya (FIFA) ta fitar ranar Alhamis.

Super Eagles, wacce a yanzu take matsayi na 33 a duniya kuma ta uku a Afirka, ta kasance ta 36 a duniya kana ta biyar a cikin watan da ya gabata, Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan

Al'ajabi: Yadda tsohuwa ta mutu a zaune akan teburi ba a sani ba tsawon shekaru 2

Kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ta haura sama
Ci gaba: Duk da shan lallasa a kofin AFCON, Super Eagles ta haura sama a 2022 | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: Getty Images

Kasashen da suka tabuka alheri a gasar AFCON

Sabuwar kungiyar da ta lashe gasar AFCON, kasar Senegal ba ta tawaya ba, sai dai ma ci gaba da rike matsayinta na mafi girma a Afirka ba, kuma ta tashi daga matsayi na 20 zuwa 18 a jerin kasashen duniya, kamar yadda Pulse ta tattaro.

Wannan shi ne matsayi mafi girma da Teranga Lions suka taba samu, wadanda har yanzu suke murnar nasarar da suka samu a gasar AFCON inda suka doke Masar da fenalti a wasan karshe.

'Yan Morocco su ne tawaga ta biyu mafi girma a Afirka kuma sun haye matsayi na 24 a duniya.

Kungiyar Atlas Lions ta kasar Moroko ta fita a gasar ne a wasan daf da na kusa da karshe na AFCON 2021, inda Masar ta lallasa ta.

Kara karanta wannan

'Yar Bokon gaske: Yadda matashiya ta kame kanta, ta kammala digiri da CGPA 7.0

Kamar yadda FIFA ta bayyana, baya ga Senegal, kasa mafi girma a Afirka a matsayi, Kamaru (38, + 12), wacce ta zo na uku a gasar cin kofin Afirka, da Masar mai matsayi na biyu (34, + 11) sun kasance mafi girman matsayi. Mahimman matakai a cikin 50 mafi matsayi.

Sauran kasashen da suka tashi da wadanda suka sauka

Sai dai kuma babban tsallen da aka gani a wannan watan shi ne na kasar Gambiya, inda kungiyar ta Scorpions ta haura matsayi na 25 zuwa matsayi na 125 bisa la’akarin da suka yi na zuwansu wasan kusa da na karshe (quarter-final) a gasar ta AFCON.

Equatorial Guinea, wacce ita ma ta kai mataki na takwas na karshe a gasar, ta haura matsayi 15, kuma yanzu tana daga cikin 100 mafi matsayi.

Sauran fitattun da suka tashi sune na Malawi (119, + 10) da Gabon (82, + 7). A nasu bangare, Mali (48, + 5) sun sami mafi girman nasarori amma duk da haka basu shiga cikin 50 mafi matsayi.

Kara karanta wannan

Tarihi a 2022: Manya-manyan laifukan kashe-kashen tsafi 4 da suka girgiza 'yan Najeriya

Sai dai abin takaicin shi ne ga Aljeriya, yadda gasar ta AFCON ta ba su kunya, ya sa kasar ta zama kasar da ta fi samun maki da ta sauka kasa warwas.

Kungiyar ta kasar Aljeriya mai suna The Desert Foxes ta sauka daga matsayi na 14 zuwa matsayi na 43.

Kasashe biyar na farko a duniya sune Belgium, Brazil, Faransa, Argentina da Ingila. Za a buga sabon bayani kan kasashe na FIFA/Coca-Cola na gaba a ranar 31 ga Maris, 2022.

Najeriya tayi watsi da Baturen koci, ta fadi wadanda za su horas da 'Yan Super Eagles

A wani labarin, hukumar kwallon kafa ta Najeriya ta bada sanarwar cigaba da aiki da Austin Eguavoen a matsayin kocin tawagar Super Eagles na rikon kwarya.

Jaridar The Cable ta ce NFF ta bada wannan sanarwa ne a ranar Litinin, 7 ga watan Fubrairu 2022.

Hukumar ta NFF ta ce tayi watsi da maganar nada Jose Peseiro a matsayin sabon kocin ‘yan wasan kwallon kafa na Najeriya bayan kammala gasar AFCON.

Kara karanta wannan

Sarauniyar kyau mai Hijabi: An nemi na cire Hijabi don na ci nasara, amma na tubure

Asali: Legit.ng

Online view pixel