AFCON: Kocin Najeriya ya fadi babban dalilin da ya sa Tunisiya ta yi waje da S/Eagles

AFCON: Kocin Najeriya ya fadi babban dalilin da ya sa Tunisiya ta yi waje da S/Eagles

  • Augustine Eguavoen ya yi magana a game da yadda aka fatattaki Najeriya daga gasar AFCON 2021
  • Kocin na Super Eagles yana ganin Alkalin da ya busa wasan Najeriya da Tunisiya bai yi adalci ba
  • Eguavoen ya na so ‘yan wasan Super Eagles su manta abin da ya faru, su fara shiryawa kasar Ghana

Cameroon - A ranar Lahadi, 23 ga watan Junairu 2020, kocin rikon kwarya na Super Eagles, Augustine Eguavoen ya bayyana dalilin rashin nasarar da suka samu.

Jaridar Punch ta rahoto Augustine Eguavoen yana cewa bai dace kasar Tunisiya tayi waje da Najeriya a zagayen kasashe 16 na gasar cin kofin Afrika na AFCON ba.

An fatattaki ‘yan wasan kwallon kafan Najeriya daga gasar bayan Tunisiya ta doke su da ci 1-0.

Kara karanta wannan

AFCON 21: Sanata ba zai ci abinci ba, da martanin jama’a bayan yin waje da Najeriya

Da yake magana da manema labarai bayan wasan, Eguavoen ya bayyana cewa ba ayi alkalanci mai kyau a wasan na su da Tunisiya ba, hakan ya jawo aka fitar da su.

Kocin rikon kwaryan na Super Eagles, Eguavoen ya ce ‘yan kwallon na sa sun yi bakin kokarinsu. Jan katin da Alex Iwobi ya samu daga shigowarsa ne ya yi masu cikas.

S/Eagles
'Yan wasan Super Eagles Hoto: Bukola Saraki / Facebook
Asali: Facebook

“Mun yi yunkurin rama kwallon da aka zura mana bayan Tunisiya sun jefa mana kwallo a raga.”
“Sai kuma mu ka samu jan kati. “Ya bayyana a zahiri cewa ba ayi busa na adalci ba.” - Augustine Eguavoen

Ba zan ce komai ba, a tari gaba

“Ba zan soki Alkalin wasan ba, saboda sun kware a kan aikinsu. Amma Alex Iwobi bai cancanci jan katin da aka ba shi ba. Ba da gangan ya yi dukan ba.” - Augustine Eguavoen

Kara karanta wannan

Takarar shugaban kasa a 2023: Babatu 3 da Tinubu ya yi da ka iya sa ya fadi a 2023

Kocin mai shekara 56 ya fadawa ‘yan kwallon su hakura da abin da ya faru a filin wasan Roumde Adjia da ke Garoua a kasar Kamaru, su fara shiryawa Qatar 2022.

Mai horas da ‘yan wasan yana so Super Eagles su manta abin da ya faru, su fara shiryawa wasan da za su buga da kamaru domin samun zuwa gasar cin kofin Duniya.

An rasa N100m

A makon jiya ne aka ji cewa fitaccen Attajirin kasar nan, Femi Otedola ya sa kyautar kudi har Dala $250,000 ga Super Eagles idan suka samu nasara a gasar bana.

Idan ‘yan wasan suka dawo gida da kofin AFCON, mai kudin zai ba su kusan N102m. A halin yanzu 'yan wasan ba za su samu kudin ba tun da aka yi waje da su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel