AFCON: Babban Attajirin Afrika, Otedola ya yi wa Super Eagles alkawarin fiye da N100m

AFCON: Babban Attajirin Afrika, Otedola ya yi wa Super Eagles alkawarin fiye da N100m

  • Fitaccen Attajirin kasar nan, Femi Otedola ya sa kyautar kudi har Dala $250,000 ga Super Eagles
  • Idan ‘yan wasan Najeriya suka dawo gida da kofin AFCON 21, mai kudin zai ba su kusan N102m
  • Gwamnan CBN ya fadawa ‘yan kwallon cewa za a raba masu $50, 000 a kan duk kwallon da suka ci

Shahararren ‘dan kasuwar nan, Femi Otedola ya yi alkawarin zai bada kyautar $250,000 ga ‘yan wasan Najeriya idan suka lashe gasar AFCON 21.

A ranar 21 ga watan Junairu 2022, Punch ta fitar da rahoto cewa Femi Otedola zai bada wadannan kudi idan Super Eagles suka dawo gida da kofin.

Adadin kudin da ‘dan kasuwan zai ba ‘yan kwallon ya kai Naira miliyan 102 a kudin Najeriya.

Kara karanta wannan

AFCON: Duk da ya na jirgi a hanyar dawowa daga Gambia, Buhari ya tuna da Super Eagles

Jaridar ta ce baya ga haka, ‘yan kwallon za su samu N49,389,600 ($120,000) a matsayin kyautar kwallaye har shida da suka zura a zagaye na rukuni.

Kungiyar Coalition Against COVID-19 da aka kafa domin yakar Coronvairus wanda aka fi sani da CACOVID za ta ba taurarin kyauta saboda kokarinsu.

AFCON
Tawagar Super Eagles Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

CACOVID sun yi alkawarin bada kyautar $20,000 a kan duk wata kwallo da ‘yan wasan Super Eagles suka zura a zagayen farko na wasannin rukuni.

Godwin Emefiele ya ziyarci Kamaru

Gwamnan babban bankin Najeriya na CBN, Godwin Emefiele ya wakilci CACOVID a lokacin da ya kai wa ‘yan wasan ziyara a kasar Kamaru a yammacin jiya.

Godwin Emefiele ya yi wa ‘yan wasan albishir da sakon CACOVID, ya ce yanzu za a rika bada kyautar $50,000 kan duk wata kwallo da Najeriya ta ci.

Kara karanta wannan

EFCC ta na binciken mutum 5 a cikin masu neman hawa kujerar Shugaban jam’iyyar APC

“Daga yanzu duk wata kwallo da ku ka zura a raga, kun ci kyautar fam Dala $50,000.”
“Shi ma Femi Otedla wanda yana cikin ‘Yan CACOVID, ya fadi mani cewa idan ku ka yi nasara, ya ajiye maku $250,000 a baki. Wannan kadan ma kenan.”

- Godwin Emefiele

Baya ga haka akwai irinsu Allen Onyeama wanda ya ba Super Eagles N10m bayan doke Masar. Attajirin zai ba 'yan wasan N50m idan suka lashe gasar bana.

Najeriya v Tunisiya

An hada Tunisiya da Najeriya a zagaye na gaba a za a buga a gasar AFCON na shekarar nan. Za a hadu a a ranar Lahadi a babban filin Kamaru na Roumde Adjia.

Super Eagles sun saba lallasa Kasar Tunisiya a tarihi, wannan ne zai zama haduwarsu na biyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel