Hukumar NFF ta fatattaki kocin Super Eagles, Rohr, ta dawo da tsohon kocin da ya tashi a 2007

Hukumar NFF ta fatattaki kocin Super Eagles, Rohr, ta dawo da tsohon kocin da ya tashi a 2007

  • Hukumar kula da harkar kwallon kafa ta NFF ta bada sanarwar korar babban koci, Gernot Rohr
  • NFF tace tsohon kyaftin kuma koci a da, Augustine Eguavoen, zai cigaba da horas da Super Eagles
  • Eguavoen wanda ya taba zama gwarzon nahiyar Afrika a 1994 zai yi aiki tare da su Yusuf, Yobo

Abuja - Hukumar kula da harkar kwallon kafa a Najeriya, NFF ta tsige kocin kungiyar Super Eagles, Gernot Rohr, ta kuma nada Augustine Eguavoen.

Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Lahadi, 12 ga watan Disamba, 2021, cewa NFF ta sallami Gernot Rohr bayan ya yi shekaru biyar ya na wannan aiki.

Babban sakataren hukumar NFF, Dr. Mohammed Sanusi ya fitar da jawabi ya na cewa tsohon ‘dan wasan Najeriya, Eguavoen, ya sake dawowa kujerar koci.

Kara karanta wannan

Bayan shekaru 2 ana wahala, Bill Gates ya fara hango karshen annobar annobar COVID-19

Jawabin hukumar NFF

“Alakar hukumar kwallon kafan Najeriya da Mista Rohr ya zo karshe. Mu na gode masa a game da kokarin da ya yi wa Super Eagles da Najeriya.”
“Mu na kuma so mu godewa ma’aikatar wasanni da matasa da goyon-bayan da ta rika ba mu.” - Mohammed Sanusi.
Kocin Super Eagles, Rohr, ta dawo da tsohon kocin da ya tashi a 2007
Tsohon kocin Super Eagles, Gernor Rohr Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Rohr mai shekara 68 a Duniya, ya yi kusan shekaru biyar da watanni hudu ya na koci. Hakan yana nufin babu wanda ya kai shi dadewa a wannan kujera.

Augustine Eguavoen wanda yanzu haka shi ne darektan kula da wasanni zai karbi ragamar horas da ‘yan kwallon Super Eagles a matsayin kocin rikon kwarya.

Goal yace shugabannin NFF sun cin ma wannan matsaya ne bayan wani taro da suka yi a jiya.

Abokan aikin Augustine Eguavoen

Kara karanta wannan

Da duminsa: Gwamnati ta bukaci wadanda sukayi rigakafin Korona sau 2 su je a kara musu na 3

Sanarwar tace Eguavoen zai yi aiki da Salisu Yusuf a matsayin babban koci da Paul Aigbogun, Joseph Yobo da Terry Eguaoje a matsayin mataimakan koci.

Hukumar tace Eguavoen zai yi aiki da Aloysius Agu a matsayin mai kula da masu tsaron raga.

Tsofaffin ‘yan wasan Najeriya Jay Jay’ Okocha, Nwankwo Kanu da Garba Lawal za su taimaka wajen horas da ‘yan wasan da zama jakadu na Super Eagles.

'Yar kwallon Najeriya ta koma direba

A makon da ya wuce aka ji labarin tsohuwar 'yar kwallon Najeriya, Rachael Aladi Ayegba ta zama mai tuka motoci, yanzu ta koma sana’ar tukin bas a Birtaniya.

Rachael Aladi Ayegba mai shekara 35 tayi ritaya daga kwallon kafa, ta koma sana'ar tukin mota.

Asali: Legit.ng

Online view pixel