Duniya tayi wa tsohuwar ‘Yar kwallon kafar Najeriya tutsu, ta zama direbar babbar mota a Ingila

Duniya tayi wa tsohuwar ‘Yar kwallon kafar Najeriya tutsu, ta zama direbar babbar mota a Ingila

  • Rachael Aladi Ayegba ta zama mai jan motoci, yanzu ta koma sana’ar tuka bas a can kasar Birtaniya
  • Tsohuwar ‘yar kwallon tace a yanzu ta daina shiga tsakanin ragar kwallon kafa saboda tsufa ya zo
  • A wata hira da aka yi da ita, tsohuwar ‘yar wasar mai shekara 35 tace tukin mota sai an yi hattara

England - Wani rahoto daga Punch yace tsohuwar ‘yar wasan kwallon kafan Najeriya, Rachael Aladi Ayegba ta zama direbar mota a kasar Ingila.

Rachael Aladi Ayegba wanda ta ke tsaron raga a lokacin da ta ke wasa ta fadawa jaridar nan ta Evening Standard ta Birtaniya cewa ta koma tukin bas 185.

Tsohuwar ‘yar kwallon mai shekara 35 a Duniya, ta ajiye harkar kwallo a yau, ta koma tukin mota kirar bas daga yankin Lewisham zuwa Victoria a Ingila.

Kara karanta wannan

Dala daya (N409.89) na biya kudin sadaki, Matashin da ya auri yar shekara 70

A hirar da tayi da ‘yan jarida, Ayebga ta bayyana cewa yanzu tayi ritaya daga kwallo, sannan ta kuma bayyana cewa tukin motar da take yi, ya fi kwallo wahala.

Tsohuwar ‘yar kwallon take cewa ana iya yin kuskure a wajen wasan kwallo saboda akwai wasu 'yan wasan. Amma a tuki, ran mutane su na hannun mutum.

Tsohuwar ‘Yar kwallo
Rachael Aladi Ayegba Hoto: www.standard.co.uk
Asali: UGC

Tukin 185 bas na yi ne - Rachael Ayegba tayi

“Idan ka na tuka bas, to shikenan, ta kanka, kake yi.”
“A bas, dole sai ka shirya 100%, a kwallo kuwa, idan kai mai tsaron raga ne, ‘yan wasan baya za su iya taimaka maka. Amma ba a yin kuskure wajen tuka bas."
“Na zama tsohuwa. Dole ka san lokacin da ya kamata ka dakata.” - Rachael Ayegba ta bar kwallo

Kara karanta wannan

An kashe mana mutum 80 a dare 1 – Manyan Sokoto sun aikawa Buhari wasika mai ban tausayi

Ayegba ta shaidawa manema labarai cewa babu ‘dan wasan kwallon kafan da take sha’awa irin tsohon ‘dan wasan kungiyar Real Madrid, Cristiano Ronaldo.

Tarihin wasan Rachael Ayegba

A lokacin da ta ke buga wasan kwallon kafa, Rachael Ayegba ce ta tsare ragar Super Falcons a gasar cin kofin Duniya na mata da aka yi a shekarar 2007.

Haka zalika tsohuwar tauraruwar ta Super Falcons ta bugawa Najeriya a gasar cin kofin kasashen Afrika na mata da aka shirya a shekarun 2007 da kuma 2008.

A lokacin da take wasa Ayegba ta bugawa kungiyar PK-35 Vantaa na tsawon shekara da shekaru. ‘Yar wasan ta Najeriya tayi nasarar lashe gasar Finland a 2013.

Asali: Legit.ng

Online view pixel