UCL: Jerin Kungiyoyi 16 da su ka isa mataki na gaba yayin da aka fatattako Barcelona

UCL: Jerin Kungiyoyi 16 da su ka isa mataki na gaba yayin da aka fatattako Barcelona

  • An gama buga dukkanin wasannin zagayen farko na gasar cin kofin nahiyar Turai a cikin makon nan
  • Kungiyoyi irinsu Ajax, Liverpool da Bayern sun samu maki 18 bayan sun yi nasara a duka wasannin
  • Wannan karo Barcelona za ta buga Europa League yayin da aka yi waje da kungiyar AC Milan gaba daya

Europe - An kammala zagayen farko na wasannin gasar cin kofin Turai. A halin yanzu za a jira kungiyar UEFA ne ta fitar yadda zagaye na biyu zai kasance.

Yadda tsarin yake kuwa shi ne a cikin kowane rukuni, akwai kungiyoyin kwallo kafa biyu da za su fito. Wanda ya zo na uku zai tafi gasar karamin kofin UEFA.

Duk kulob din da ya yi rashin sa’a ya zo na karshe a zagayen farkon, ya fita daga gasar kenan. Akwai rukunai takwas, ma’ana kungiyoyi 16 ne za su tsallaka.

Kara karanta wannan

Mako Ɗaya Bayan Miƙa Rayuwarsu Ga Yesu, Matasa 2 Sun Kashe Fasto a Cikin Coci a Legas

Kamar yadda aka wallafa a shafin UEFA, a ranar Litinin ne za a san kungiyoyin da za su gwabza da juna a wannan zagaye na gaba da zai kankama bayan hutu.

Legit.ng ta fara da jerin kulob din da suka zo na farko a rukuninsu. Daga ciki akwai wadanda suka yi nasara a duka wasanninsu irinsu Ajax, Bayern da Liverpool.

Jerin Kungiyoyi 16
Kungiyoyin da suka fito UCL Hoto: ww.uefa.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Su wanene su ka zo na daya a rukunansu?

1. Manchester City

2. Liverpool

3. Ajax

4. Real Madrid

5. Bayern Munich

6. Manchester United

7. Lille

8. Juventus

Kungiyoyin da suka zo na biyu a bana

1. Paris Saint-Germain

2. Atletico Madrid

3. Sporting Lisbon

4. Inter Milan

5. Benfica

6. Salzburg

7. Chelsea

8. Villareal

A karon farko cikin shekaru sama da 15, an yi waje da Barcelona tun a yanzu, kungiyar za ta koma buga gasar Europa League ne idan an dawo wasa a shekarar badi.

Kara karanta wannan

Bayan shekaru 2 ana wahala, Bill Gates ya fara hango karshen annobar annobar COVID-19

Gasar Ballon d'or 2021

A makon da ya gabata ne aka ji cewa Lionel Messi ya tashi da kyautar Ballon d’Or na wannan shekarar, ya doke Robert Lewandowski duk da irin kokarin da ya yi.

Tun daga nan wasu daga cikin 'yan wasan kungiyar Bayern Munich su ka sha alwashin fanshe takaicinsu a kan tsohuwar kungiyar Lionel Messi watau Barcelona.

Asali: Legit.ng

Online view pixel