Abin da ya sa na doke Robert Lewandowski a tseren Ballon d’or 2021 – Lionel Messi

Abin da ya sa na doke Robert Lewandowski a tseren Ballon d’or 2021 – Lionel Messi

  • Lionel Messi ya tashi da kyautar Ballon d’Or na wannan shekarar, ya doke Robert Lewandowski
  • ‘Dan wasan na Paris Saint Germain yace ya lashe wannan kyauta ne saboda ya ci gasar Copa America
  • Messi ya jagoranci kasar Argentina ga babbar nasarsu a kwallon kafa na karon farko tun shekarar 1993

Paris - Lionel Messi ya yi magana game da nasarar da ya samu na lashe kyautar Ballon d’Or na shekarar 2021, wanda wannan ne karonsa na bakwai.

Jaridar Punch ta rahoto Lionel Messi mai shekara 34 a Duniya ya na alakanta nasarar da ya samu da gasar Copa America kasar Argentina ta lashe a bana.

Lionel Messi ne ya zama gwarzon ‘dan wasan Duniya, yayin da Alexia Putellas ta ci kyautar mata.

Kara karanta wannan

'Yan APC mashaya barasa ne, su suke sukar ayyuka na a Benue, gwamna Ortom

Messi a jawabinsa, ya yarda cewa ‘dan wasan gaban kungiyar Bayern Munich, Robert Lewandowski ya cancanta ya ci wannan kyauta a 2020.

Duk da ya bar Barcelona, ya koma Paris Saint Germain, AFP ta ce Messi bai samu matsala ba a dalilin jagorantar Argentina ga lashe kofi a shekar bana.

Lionel Messi
Lionel Messi da Ballon d'Or Hoto: www.fourfourtwo.com
Asali: UGC

Menene sirrin Messi?

“Shekaru biyu da suka wuce, na yi tunanin wasa na ya zo karshe, amma ga shi kuma na dawo nan.”
“Mutane su na tambaya ta yaushe zan yi ritaya, amma yanzu ga ni a Faris, kuma ina jin dadi sosai.”
“Ban san shekaru nawa su ka rage mani ba, amma ina fatan da yawa domin ina jin dadin abin da na ke yi.”
“Abin da na yi da Argetina dogon burina ne ya tabbata. Ina tunanin na ci wannan kyauta ne saboda abin da mu ka yi a gasar Copa America.”

Kara karanta wannan

Gwamnan Benue: Ubangiji ne ya zo min yace na sake tsayawa takarar gwamna

“Saboda haka na sadaukar da kyautar ga abokan wasa na.” – Lionel Messi.

Messi ya ci Ballon d'Or na 7

Messi wanda ya lashe Ballon d’Or a 2009, 2010, 2011, 2012, 2015 da 2019 ya jagoranci kasarsa ga lashe kofin farko a birnin Rio de Janeiro a cikin shekara 28.

A daren Talata ne Messi ya zama gwarzon Duniya, manyan ‘yan wasan gaban Foland da Faransa, Robert Lewandowski da Karim Benzema sun biyo shi a baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel