Messi ya yi magana game da gabarsa da Ronaldo a Sifen da komawarsa kungiyar Man Utd

Messi ya yi magana game da gabarsa da Ronaldo a Sifen da komawarsa kungiyar Man Utd

  • Lionel Messi ya yabawa halin Cristiano Ronaldo bayan komawarsa kungiyar Manchester United
  • Babban ‘Dan wasan yace tsohon ‘dan wasan na Real Madrid bai sha wahalar sabawa da Ingila ba
  • Tauraron na Paris Saint-Germain yace Manchester United za ta fito daga gargadar da ta ke ciki a BPL

Paris - Babban ‘dan wasan Duniya, Lionel Messi ya yi magana a game da komawar Cristiano Ronaldo tsohuwar kungiyarsa ta Manchester Uta ta Ingila.

‘Dan wasan da ya shafe kusan duka shekarun kwallonsa a Barcelona, ya tattauna da Marca a game da zuwan Ronaldo Ingila da alakar da ke tsakaninsu.

Goal.com ta rahoto cewa Lionel Messi ya yabi Cristiano Ronaldo da ya zanta da jaridar Marca.

Kara karanta wannan

Rikicin gida ya jawo Jigon APC ya tona asirin abin da ya faru a zaben Abba v Ganduje a 2019

Ronaldo ya cigaba da cin kwallayensa - Messi

“Cristiano ya riga ya san kulob din, amma yanzu abubuwa sun canza, an shiga sabon fai-fai, kuma har ya saba daga zuwansa, ya saje da kyau.” – Messi.
“Tun da farko, ya ci kwallaye kamar yadda ya saba, bai samu matsalar sabo ba.”

Tangardar Man Utd a gasar Firimiyar bana

‘Yan jaridar sun yi wa Lionel Messi tambaya game da tasgaron da Manchester United ta ke samu a gasar Firimiya bayan ta sha mugun kashi a hannun Watford.

Messi da Ronaldo a UCL
Messi da Ronaldo a shekarar bara Hoto: en.as.com
Asali: UGC

‘Dan wasan na kasar Argentina mai bugawa PSG a yanzu yace Man Utd za ta dawo da karfinta nan da karshen shekara kamar yadda aka san gasar Ingilar.

“(Manchester) United kungiya ce mai karfi da kwararrun ‘yan kwallon kafa.”

Kara karanta wannan

Jerin Koci 7 da aka sallama daga aiki yayin da Cristiano Ronaldo ke taka leda a karkashinsu

“Gasar firimiya ta na da wahala, abubuwa su na iya canzawa farat daya, an saba yin haka.”
“Bayan watan Disamba, abubuwa da yawa na canzawa, komai na iya faruwa.” – Messi.

Messi ya na kewan Ronaldo?

“Abu ne ban-kaye gare mu da sauran mutane saboda mun ji dadi sosai. Abu ne da za a tuna da shi, ba zai bar tarihin kwallon kafa.” - Messi a kan zamansa da Ronaldo a Sifen.

Kawo yanzu Cristiano Ronaldo mai shekara 36 a Duniya ya ci kwallaye kimanin goma daga zuwansa Manchester daga kungiyar Juventus a kakar shekarar nan.

Amma kun ji cewa duk da kokarin Ronaldo, an sallami Ole Gunnar Solskjaer daga aikinsa a kungiyar kwallon kafa ta Manchester United saboda rashin kokari.

Kungiyar ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta a Instagram a makon jiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel