Matashin ‘Dan wasa mai shekara 23 da ya fi su Messi, Neymar da Cristiano Ronaldo kudi

Matashin ‘Dan wasa mai shekara 23 da ya fi su Messi, Neymar da Cristiano Ronaldo kudi

  • Duk da cewa bai yi suna sosai a Duniya ba, da wuya a samu ‘dan kwallon da ya fi Faiq Bolkiah kudi
  • Ana tunanin Bolkiah ya mallaki sama da Dala biliyan 20, kimanin Naira tiriliyan 8 kenan a Najeriya
  • ‘Dan wasan na kungiyar Marítimo ‘da ne ga Sarkin kasar Brunie, Mai martaba Hassanal Bolkiah

England - Ana ganin cewa babu wanda ya sha gaban Lionel Messi da Cristiano Ronaldo a cikin ‘yan kwallon kafa idan ana maganar kwarewa da dukiya.

Sai dai akwai Faiq Bolkiah mai shekara 23 wanda ana tunanin ya dama su, ya shanye a arziki. The Sun tace Bolkiah yana zaman jiran gadon fam biliyan £13.

‘Dan wasan mai bugawa kungiyar Maritimo a kasar Portugal yana cikin wadanda za su gaji Sarkin kasar Brunie, Hassanal Bolkiah, da zarar ya kwanta dama.

Rahoton jaridar kasar Ingilar yace an haifi Bolkiah ne a birnin Los Angeles a kasar Amurka, don haka yake da takardar zama ‘dan kasar Amurka da kuma Brunei.

‘Dan kwallon ya yi karatu ne a makarantar Bradfield College da ke kasar Birtaniya. Ana kyautata zaton cewa yanzu haka ya ba akalla fam Dala biliyan 20 baya.

Mahaifin ‘dan wasan, Jefri Bolkiah shakiki ne ga Sarkin Brunie, wanda yana cikin attajirin Duniya. Shi kuwa Faiq ‘dan gado ne wanda aka haifi cikin dukiya.

Matashin ‘Dan wasa
Faiq Bolkiah a Chelsea Hoto: www.dailystar.co.uk
Asali: Getty Images

A wasu kulob Bolkiah ya buga kwallo?

A shekarar 2009 ne Faiq Bolkiah ya rattaba hannu a kwantiragin shekara guda da kungiyar Southampton F.C. Bai bar kulob din ba sai a karshen 2011.

Bolkiah ya kuma bugawa matasan kungiyar Arseanl a 2013 a gasar cin kofin Lion City – da shi aka gwabza da Corinthians, Eintracht Frankfurt, da PSV.

A 2014 aka ji cewa ‘dan wasan gefen ya samu kwangilar shekara biyu da kungiyar Chelsea.

Bayan yunkurin zuwansa kungiyar Stoke City bai yiwu ba, sai ya koma tafi kungiyar Leicester City a 2016. A kungiyar ya cigaba da taka leda har zuwa 2019.

A shekarar da ta gabata ne aka ji Bolkiah ya bar Ingila, ya koma Marítimo a Portugal, yanzu haka yana buga wasa, ko da yake ba dole saboda kudi yake kwallo ba.

Messi da Ronaldo sun fi kowa yin kudi da kwallo

A shekarar bara aka bayyana Lionel Messi a matsayin tauraron da ya fi kowa samun kudi da kwallo. A lokacin ‘dan wasan ya sha gaban har Cristiano Ronaldo.

Tun ba yau ba dai Lionel Messi da Cristiano Ronaldo ne sahun gaba a jerin attajiran 'yan kwallo. A yau babu 'dan wasa mai samun kudi da Instagram irin Ronaldo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel