Kano: Alƙalin Kotun Shari’ar Musulunci Ya Aike da Alhassan Yusuf Gidan Ɗan Kande Saboda Satar Kare

Kano: Alƙalin Kotun Shari’ar Musulunci Ya Aike da Alhassan Yusuf Gidan Ɗan Kande Saboda Satar Kare

  • Wata kotun shari'a da ke zamanta a Fagge jihar Kano ta tura wani matashi Alhassan Yusuf gidan yari
  • Hakan ya biyo bayan matashin ya amsa cewa ya kutsa gidan wani mutum ne a Tudin Maliki Quaters ya sake masa kare
  • Mai gabatar da kara Mr Abdul Wada ya ce kudin karen ya kai N10,000 kuma laifin da Yusuf ya aikata ya saba wa shari'a

Jihar Kano - Wata kotun shari'a da ke zamanta a Fagge, a ranar Laraba ta bada umurnin a kai wani Alhassan Yusuf mai shekaru 21 gidan gyaran hali, NewsWireNGR ta ruwaito.

Hakan ya faru ne bayan ya amsa laifinsa na satar wani kare da aka kiyasta kudinsa ya kai N10,000.

An tuhumi wanda ake tuhumar, mazaunin Tudun Maliki Quaters a karamar hukumar Kumbotso da laifuka biyu masu alaka da kutse da sata.

Kara karanta wannan

Jagoran APC a Neja ya shawarci Buhari da ya tsige Lai Mohammed daga kujerar minista

Kano: Alƙalin Kotun Shari’ar Musulunci Ya Aike da Alhassan Yusuf Gidan Ɗan Kande Saboda Satar Kare
Kano: Alƙalin Kotun Shari’ar Ya Aike Da Alhassan Yusuf Gidan Ɗan Kande Saboda Satar Kare. Hoto: NewsWireNGR
Asali: Twitter

Ya amsa laifinsa nan take yayin da aka karanto masa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Alkalin kotun, Dr Bello Khalid, ya bada umurnin a bawa wanda ake zargin matsuguni a gidan gyaran hali.

Jaridar ta rahoto cewa ya daga cigaba da shari'ar har zuwa ranar 3 ga watan Disamba.

Yadda abin ya faru

Tunda farko, Mai gabatar da kara, Mr Abdul Wada, ya sanar da kotu cewa wanda aka yi karar ya aikata laifin ne a ranar 8 ga watan Nuwamba a Tudun Maliki Quaters, Kano.

Ya ce misalin karfe 5.40 na yamma, wanda aka yi karar ya kutsa gidan wani Najib Shehu da ke Tudun Maliki Quaters.

Wada ya ce karen na Shehu ya kai N10,000.

Wada ya ce laifin ya ci karo da sashi na 133 na dokar shari'a ta jihar Kano.

Kano: Mata ta garzaya kotun shari'a ta nemi a raba aurenta da mijinta saboda murguɗa baki

Kara karanta wannan

Kano: Shugaban Karamar Hukuma Ya Jagoranci Matasa Sun Rusa Aikin Gini Da Dan Majalisa Ke Yi

A wani labarin, mata ta maka mijin ta gaban kotu don bukatar a raba auren su sakamakon yadda rikici da tashin hankali ke aukuwa tsakanin su.

Ta bayyana gaban Alkali Munzali Tanko na kotun musulunci da ke zama a Kofar Kudu a birnin Kano don gabatar da korafin ta bisa ruwayar Dala FM.

Kamar yadda ta ce, mijin na ta ya na ci wa iyayen ta mutunci kuma ba ya ganin darajar su ko kadan kamar yadda ya zo a ruwayar na Dala FM.

Asali: Legit.ng

Online view pixel