Messi ya doke Ronaldo, ya zama ‘Dan kwallon da ya fi kowa samun arziki
An bayyana Lionel Messi a matsayin ‘dan wasan kwallon kafan da ya fi kowa kudi – Hakan ya na nufin ‘dan wasan ya sha gaban Cristiano Ronaldo.
France Football ta tattaro sunayen ‘yan kwallon Duniya da su ka fi arziki a shekarar 2019. An samu Lionel Messi da Cristiano Ronaldo a kan sahun gaba.
Lionel Messi ya samu fam miliyan £120 a shekarar da ta gabata, wannan kudi ya zarce abin da Cristiano Ronaldo ya samu a Juventus da fam miliyan £11.
A cikin ‘yan kwallon kafa, Taurarin nan biyu ne kawai su ka tara abin da ya haura fam miliyan £100 a shekara guda daga albashi, alawus da harkar talla.
‘Dan wasan kungiyar PSG, Neymar Jr. wanda ya tada kai da £87m a bara shi ne ya zo na uku a jerin. Akwai tazarar akalla fam £22m tsakaninsa da Ronaldo.
KU KARANTA: 'Dan wasan Barcelona ya kamu da COVID-19
Gareth Bale wanda ya ke fuskantar barazana a Real Madrid shi ne na hudu a wannan jeri. A shekarar bara ‘dan wasan na kasar Wales ya tara £35.45m.
Antoine Griezmann wanda ya tashi daga Madrid zuwa Barcelona ya samu shiga cikin sahun attajiran ‘yan wasa biyar na Duniya da kimanin fam £35.25m.
Ragowar ‘yan wasan da mu ke tunanin su na biye a bayan wadannan taurari su ne Raheem Sterling na Liverpool, Kylian Mbappe, na PSG da Eden Hazard.
Ga dai yadda jerin ya ke:
1. Lionel Messi - £120m
2. Cristiano Ronaldo - £109m
3. Neymar - £87m
4. Gareth Bale - £35.45m
5. Antoine Griezmann - £35.25m
6. Eden Hazard - £32.06m
7. Andres Iniesta - £31.14m
8. Raheem Sterling - £30.96m
9. Robert Lewandowski - £26.56m
10. Kylian Mbappe - £24.73m
A jiya kuma aka ji cewa kungiyar Leipzig ta bada mamaki, ta yi waje da Atletico Madrid daga gasar Zakarun Turai da ci 2-1.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng