Jihar Zamfara
Ayyukan yan ta'adda ya yi kamari a yankin Arewacin kasar nan, inda aka aka sace mutane akalla 7568 a cikin shekara daya kawai, lamarin da ya sa aka fara ramawa.
Jihohin Arewa da dama na fuskantar matsalolin garkuwa da mutane musamman a bangaren Yammaci wanda ya daidaitasu tare da kawo cikas a tattalin arzikinsu.
Hedkwatar tsaro ta kasa (DHQ) ta fito ta yi magana kan ikirarin da 'yan bindiga suka yi na kwace motoci masu sulke na dakarun sojojin Najeriya a jihar Zamfara.
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya yi tattaki zuwa karamar hukumar Gummi inda ambaliya ta ritsa da su. Ya ba da tallafin kudi da filaye ga wadanda abin ya shafa.
Ambaliyar ruwa ta shafi mutane masu yawa a jihar Zamfara. Sama da mutum 10,000 ne suka rasa matsugunansu. Gwamnan jihar ya yi jajen aukuwar hakan.
A cikin wani bidiyo da aka wallafa, an gano dan ta'adda Bello Turji da yaransa suna shewa bayan samun iko da motocin sulke na sojoji guda biyu a daji.
Mutanen gari a ƙauyen Matusgi da ke ƙaramar hukumar Talata Mafara a jihar Zamfara sun yi fito na fito da 'yan bindiga. Sun hallaka mutum 37 har lahira.
Rundunar yan sanda ta zargi sojan Najeriya da harbe shugaban yan sandan Wasagu, Halliru Liman har lahira yana kan hanya zuwa Birnin Kebbi daga jihar Zamfara.
Wani rahoto mai zaman kansa ya tuhumi gwamnonin Zamfara da Kano, Dauda Lawal da Abba Kabir Yusuf a matsayin wadanda ake zargi da daukar nauyin zanga zangar yunwa.
Jihar Zamfara
Samu kari