Jihar Sokoto
Mun ji cewa Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya nemi mutane su yi addu’ar zaman lafiya a Najeriya. Gwamnan ya kuma yi wa mutanensa alkawari a sakon barka da sallah da ya fitar.
Wata matashiya yar Najeriya ta kafa tarihi kwanan nan yayinda ta zama shugabar kungiyar dalibai ta farko mace a wani makarantar jami’a da ke yankin arewacin kasar.
Rahotanni sun kawo cewa wasu yan bindiga dauke da makamai sun tashi garuruwa sama da 70 a jihar Sokoto, yayin da suka kashe mutane da dama tare da sace tarin dukiya da suka hada da dabbobi.
A ranar Juma'a 26 ga watan Yulin, birnin Shehu wato jihar Sakkwato, ya tumbatsa da manyan kasar nan a wajen halartar daurin auren dan wakilin shiyyar Kano ta Arewa a zauren majalisar dattawa, Sanata Kabiru Gaya.
Rahotanni sun kawo cewa wasu yan bindiga sun kai farmaki a wasu kauyuka da ke karkashin karamar hukumar Goronyo ta jihar Sokoto, inda suka kashe mutane 29.
Rahotanni sun kawo cewa wasu da ake zargin yan bindiga ne sun kashe sama da mutane 20 a kauyen Dan Tatsako da ke karamar hukumar Goronyo na jihar Sokoto.
Mun samu labari cewa kotun zabe ta yi waje da shari’ar ‘Dan takarar PDP a Sokoto. ‘Dan takarar PDP na Mazabar Wurno ya fitar da kararsa daga Kotu wanda ya sa a ka kotu ta biya sa kudi.
A wani zance da ya fito daga hannun Darakta Janar na yada labarai da al’amuran yau da kullum na gwamnan, Abubakar Shekara ya sanar cewa “daga cikin sabbin kwamishinonin akwai tsohon dan majalisar Sarkin Musulmi, Alhaji Isah Bajini
Hukumar Hisbah ta jihar Sokoto ta yi nasarar damke wani direban Keke Napep, mai suna Bashar Bello dan shekarar 27 da haihuwa, a bisa zarginsa da yin garkuwa da wasu kananan yan mata guda biyu.
Jihar Sokoto
Samu kari