Sanata Alu Wamako zai gina katafaren jami’a a jahar Sakkwato

Sanata Alu Wamako zai gina katafaren jami’a a jahar Sakkwato

Tsohon gwamnan jahar Sakkwato, Sanata Alu Magatakarda Wammako ya kammala shirye shiryen gina wata katafaren jami’a mai zaman kanta a jahar Sakkwato, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Hukumar kula da jami’o’I ta kasa, NUC, ta mika takardun neman izini kafa jami’ar ga Sanata Wammako domin ya cikasu, ya kuma mayar mata dasu don ta gudanar da nazari game da cancantar yiwuwar kafa jami’ar ko akasin haka.

KU KARANTA: Gwamnatin jahar Kaduna ta ware naira biliyan 1.8 don biyan tallafin karatu

Legit.ng ta ruwaito hukumar NUC ta mika wadannan takardu ga tsohon gwamnan ne a ranar Alhamis, 22 ga watan Agusta a ofishinta dake babban birnin tarayya Abuja, yayin da ya kai ziyara ofishin.

Daga cikin jami’o’i masu zaman kansu guda 79 dake Najeriya, guda uku ne kacal suke shiyyar Arewa maso yammacin Najeriya, don haka Wammako yace manufarsa ta kafa wannan jami’a shine don cigaban matasa.

Da yake nasa jawabin, shugaban hukumar NUC kuma tsohon shugaban jami’ar Bayero ta Kano, Farfesa Adamu Rashid, ya jinjina ma kokarin Sanata Alu Wammako na samar da wannan jami’a, haka zalika Farfesan ya tuna irin gudunmuwar da Wammako ya bashi yayin da yake shugabantar jami’ar BUK.

“Za mu baka duk gudunmuwar da kake bukata wajen cimma wannan manufa ta ka na kafa jami’a, idan da za mu samu mutane 4 ko 5 masu irin wannan manufa a shugabanci da Najeriya ta yi kyau.” Inji shi.

A wani labarin kuma, mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar ya aurar da diyarsa ga dan tsohon gwamnan jahar Bauchi, Alhaji Isa Yuguda a wani kasaitaccen taro daya samu halartar jiga jigan yan siyasan Najeriya.

Daga cikin wadanda suka halarci bikin akwai Alhaji Aliko Dangote, sakataren gwamnati Boss Mustapha, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari, sarkin Bauchi, Rilwanu Suleiman Adamu, Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II, gwamnan jahar Imo, Emeka Ihedioha da dai sauran manyan mutane.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng