‘Dan takarar PDP na Mazabar Wurno ya fitar da karar da ya kai Kotu

‘Dan takarar PDP na Mazabar Wurno ya fitar da karar da ya kai Kotu

Mun ji cewa kotun da ke sauraron karar zaben jihar Sokoto ta yi wurgi da shari’ar da a ke yi da sabon kakakin majalisar dokoki na jihar watau Rt. Hon. Aminu Manya-Achida na jam’iyyar APC.

Kamar yadda Daily Trust ta rahoto, kotu ta yi waje da wannan kara ne bayan da wanda ya shigar da korafi gaban kotu watau ‘dan takarar PDP a zaben 2019, Abubakar Kwargaba, ya janye karar.

Alhaji Abubakar Kwargaba ya fadawa kotu cewa ya janye karar da ya ke yi inda ya ke kalubalantar nasarar Aminu Manya-Achida na jam’iyyar APC wanda ya lashe zaben ‘dan majalisa na Wurno.

‘Dan takarar na PDP, Abubakar Kwargaba, ya bayyanawa Alkalin kotu wannan ne ta bakin Lauyansa Yusuf Abubakar. Dokar kasa da na zabe sun bada dama mai kara ya janye karar ta sa.

KU KARANTA: Kotu na zargin Shugaban PDP da wani Limami kan laifin kisan-kai

Lauyan da ke kare Rt. Hon. Manya Achida watau Bashir Jodi ya fadawa kotu cewa ba ya adawa da janye wannan kara da a ka yi a kan sa, amma ya nemi a biya sa kudin da ya kashe N200, 000.

Shugaban masu wannan shari’a. Yusuf Ubale, ya gamsu da wannan lamari inda ya tabbatar da cewa an cire kara mai lamba ta EPT/SKT/HA/016/019 daga shari’ar zaben da a ke yi a kotun.

Mai shari’a Yusuf Ubale ya nemi a biya wanda a ka yi kara a baya watau Aminu Manya-Achida kudi har N30, 000 a dalilin abin da ya kashe wajen shari’a kamar yadda Lauyan na sa ya bukata.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng