Harin yan bindiga: An kashe mutane 29 a kauyukan Sokoto

Harin yan bindiga: An kashe mutane 29 a kauyukan Sokoto

Rahotanni sun kawo cewa wasu yan bindiga sun kai farmaki a wasu kauyuka da ke karkashin karamar hukumar Goronyo ta jihar Sokoto, inda suka kashe mutane 29.

An tattaro cewa yan bindigan sun kaddamar da hare-haren ne a ranar Laraba da ta gabata.

Mai magana da yawun yan sandan jihar Sokoto, ya tabbatar da faruwar al’amarin, yace an kasha mutane da yawa, inda yayi tir da ayyukan makasan tare da yi masu lakabi da marasa imani, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Har ila yau kakakin rundunar yace Kwamishinan yan sanda na Jihar Sokoto, Ibrahim Ka’oje ya yi alkawarin gaggauta kara matsin-lambar tsaro a jihar.

Ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyara yankunan da mahara suka yi kashe-kashen.

Shi kuma Shugaban Riko na Karamar Hukumar Goronyo, Zakari Chinaka, ya bayyana wa manema labarai a ranar Juma’a cewa ‘yan bindigan sun banka wa shaguna wuta, kuma sun saci shanu.

Ya ce maharan sai da suka shafe awa biyu cur su na barnar su yadda suka ga dama, saboda akwai matsalar tsaro a yankin.

Kauyukan, kamar yadda Chinaka ya bayyana, su na da tazarar tafiyar mota ta tsawon awa uku tsakanin su da Sokoto, babban birnin jihar.

Sannan kuma ya ce a lungu su ke, shi ya sa su ke da wahalar kai musu dauki a irin wannan mawuyacin lokaci.

KU KARANTA KUMA: Wata baiwar Allah ta rabu da mijinta saboda yafi son ta a kan mahaifiyarsa

Chinaka ya ce an kashe mutane 23 a kauyen Kamitau, wasu biyar a kauyen Ololo, sai kuma mutum daya da aka kashe a kauyen Rijiyar Tsamiya.

A wani lamari makamancin haka, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Sama da mutane 100 daga garin Jirrawa da ke karamar hukumar Kauran-Namoda a jihar Zamfara sun mamaye gidan gwamnati, Gusau dauke da wani gawa da ake zargin makiyaya ne suka kashe shi a safiyar ranar a kauyen.

Masu magana da yawun mutanen garin, Muntari Abdullahi da Muhammadu Sani sun fada ma kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) cewa yan bindigan sun kai mamaya kauyen ne da misalin karfe 10am sannan suna ta harbi a sama ba kakkautawa.

“Daga baya sai muka lura cewa sun rigada sun kashe Shafiu Inusa a gonarsa yayinda yake kokarin zuba taki a shukansa bayan ruwan sama da aka yi a daren jiya," Abdullahi yayi bayani.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel