Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: Usman Abubakar yayi luwadi da 'ya'yan uban gidanshi su 10 a jihar Sokoto

Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: Usman Abubakar yayi luwadi da 'ya'yan uban gidanshi su 10 a jihar Sokoto

- An kama wani almajiri da yake aiki a gidan wani mutumi yayi luwadi da 'ya'yan mutumin guda goma

- Almajirin ya bayyana cewa shima tun yana dan shekara 5 a duniya wani mutumi ya koya masa wannan bakar al'adar ta neman maza

- Ya ce yana rokon hukuma ta sake shi, zai je yayi ta rokon Allah ya yafe masa duka laifukan da ya aikata

Wani matashi mai shekara 21 mai suna Usman Abubakar, an kama shi da laifin yiwa yara kanana guda goma na maigidanshi luwadi, a Rungumi cikin karamar hukumar Sokoto ta Kudu, dake jihar Sokoto.

Abubakar dai da can almajiri ne kafin daga baya ya samu aiki a gidan maigidan na shi tsawon shekaru goma kenan da suka gabata.

A wata hira da yayi da manema labarai, ya bayyana cewa wani mutumi ne mai suna Malam Muntari ya koya mishi kwanciya da mazan tun yana dan shekara biyar a duniya.

KU KARANTA: Kai jama'a: Wani mutumi ya yiwa matarshi saki uku saboda gajiya da yayi da biyan kudin kitso

"Naje gidan shi nayi bara, sai yayi amfani da wannan damar yayi luwadi dani," in ji shi.

Abubakar dai ya roki a yafe masa, inda ya ce: "Idan aka sake ni, zanci gaba da rokon Allah ya yafe mini dukkan abubuwan da nayi a baya."

Shugaban rundunar masu yaki da safarar mutane, Barrister Hassan Tahir ya ce wanda ake zargin ya amsa laifinshi na kwanciya da 'ya'yan maigidan nashi guda goma.

Ya ce wanda ake zargin za a mika shi gaban kotu domin ta yanke masa hukuncin da ya dace da shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel