Yan bindiga sun kai samame jahohin Katsina da Sakkwato, sun kashe 2 sun raunata 14
Wasu gungun miyagun yan bindiga sun kai wani mummunan hari cikin kauyen Dabagi dake cikin karamar hukumar Tangaza na jahar Sakkwato, inda suka kashe mutane 2, tare da jikkata mutane 10, inji rahoton jaridar Daily Trust.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan bindigan sun kai harin ne da misalin karfe 3 na daren Litinin yayin da mutanen suke shirye shiryen taron daurin aure, kamar yadda kaakakin rundunar Yansandan jahar, ASP Muhammad Abubakar Sadiq ya tabbatar.
KU KARANTA: Katankatana: Wadume ya ambaci sunan gwamnan dake daukan nauyinsa yana ta’asa
Kaakaki Muhammad ya bayyana cewa yan bindigan sun harbe wasu matasa biyu har lahira daga cikin masu shirye shiryen bikin, sa’annan ya kara da cewa koda Yansanda suka kauyen, sun tsinci kwankon harsashin bindigar AK-47 guda 5, amma yace sun tura jami’ansu domin su bi sawun yan bindigan da nufin kamasu.
A hannu guda kuma, wasu gungun yan bindigan na daban sun kai samame a wani kauye mai suna Shimfida dake cikin karamar hukumar Jibia ta jahar Katsina a ranar Lahadin data gabata, inda suka raunata wasu mata uku da harbin bindiga.
Baya ga nan yan bindigan sun kone wasu motoci guda uku kurmus mallakin Sojoji, da guda 1 mallakin hukumar Yansandan farin kaya, Nigeria Security and Civil Defence Corps. Yan bindigan sun tare hanya ne a daidai lokacin da yan kasuwa suke komawa gida bayan kammala cin kasuwar Shimfida.
Kaakakin Yansandan jahar Katsina, Anas Gezawa ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace da misalin karfe 8 na dare suka samu labarin gungun yan bindiga sun tare hanyar kauyen Shimfida, kuma suna ta artabu da rundunar tsaron hadaka ta Sojoji da Yansanda.
Daga karshe kaakaki Anas Gezawa ya bayyana sunayen matan da suka samu rauni; Binta Umar mai shekaru 35, Jamila Ibrahim yar shekara 45 da Karima Musa mai shekaru 65, kuma sun garzaya dasu zuwa asibiti don samun kulawa.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng