Toh fah: Yan bindiga sun kai farmaki kauyuka 70 a Sokoto

Toh fah: Yan bindiga sun kai farmaki kauyuka 70 a Sokoto

Rahotanni sun kawo cewa wasu yan bindiga dauke da makamai sun tashi garuruwa sama da 70 a jihar Sokoto, yayin da suka kashe mutane da dama tare da sace tarin dukiya da suka hada da dabbobi.

An tattaro cewa mafi akasarin mazauna garuruwan da maharan suka farmawa sun samu mafaka a manyan garuruwa, domin tsiratar da rayuwarsu.

A wani zantawa da yayi da sashin RFI, Sanata Ibrahim Gobir dake wakiltar yankin, ya ce tashin hankalin ya shafi Rabah, Goronyo, Isa da kuma Sabon Birni.

Sanatan ya koka akan yadda har yanzu al’ummar yankin ke ci gaba da fuskantar barzanar hare-haren ‘yan bindigar.

KU KARANTA KUMA: Matasa sun kama wani mai garkuwa da mutane sun damkawa ‘yan sanda a Nasarawa

A wani labarin kuma Legit.ng ta rahoto a baya cewa Yan bindiga a sun kai hari kauyuka hudu a karamar hukumar Batsari dake jihar Katsina a yammacin ranar Lahadi, inda suka kashe mutane uku sannan suka yi garkuwa da mutane shida.

Kauyukan da lamarin ya cika da su, sun hada da Shingi, Sabon Garin Wagini, Hayin Nuhu da Dan Tudun Wagini.

An tattaro cewa a Shingi, an kashe babban limamin kauyen, Malam Abu Garba.Hakazalika a kauyukan Sabon Garin Wagini an kashe wasu mutane biyu masu suna Husaini Dattijo da Harisu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel