Gwamnan Sokoto ya yi kira ga Jama’a su nemi zaman lafiya a Najeriya

Gwamnan Sokoto ya yi kira ga Jama’a su nemi zaman lafiya a Najeriya

A daidai lokacin da Musulman Duniya ke murnar babbar sallah, Mai girma Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya aika sakon sallar ga daukacin Musalman da ke fadin Najeriya.

Aminu Waziri Tambuwal ya na mai kira ne ga Musulmai su dage da addu’o’in zaman lafiya a sakon idin na sa. Gwamnan ya yi wannan kira ne a Ranar Lahadi, 11 ga Watan Agusta, 2019.

Rt. Hon. Aminu Tambuwal ya ke cewa addu’o’i a wannan lokaci na musamman za su taimaka wajen kawo zaman lafiya a Najeriya. Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da jama’a ke bikin idi.

Gwamnan ya kuma nemi Musulmai su zama masu tausayi da jin-kai a a al’umma domin martabar wannan biki na idi. Waziri Tambuwal ya fadakar a kan koyi da Annabin Allah Ibrahim.

Mai girma gwamnan ya ke cewa: “Wannan lokaci ne da ke nuna bauta da imani ga Ubangiji, domin duk wata nasarar mu ta na tafe ne daga Allah madaukaki. Tambuwal ya cigaba da cewa:

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya yanka ragon layya a Garin Daura

“Albarkacin rahamar Allah ne mu ka kawo wannan rana ta yau, ina taya mutanen mu murnar idi tare da kira ga jama’a da mu zama masu mika wuya sau-da-kaf a rayuwar mu ta yau da kullum.”

“Ya zama mun dauki darasin sadaukar da kai irin na Manzon Allah Annabi Ibrahim AS."

Annabi Ibrahim shi ne wanda ya fara yanka rago a madadin ‘Dansa, wannan shi ne koyin da a ke yi yau.

"Haka kuma wannan lokaci ne da mutane za su dage da addu’o’i domin ganin an samu cigaba da zaman lafiya a daidai lokacin da a ke fama da halin rashin tsaro a kasar mu.” Inji Tambuwal.

Babban gwamnan ya nuna cewa addu’ar da Bayin Allah ke yi ya fara aiki domin kuwa an fara samun saukin matsalar tsaro. Tambuwal ya ce gwamatinsa za ta cigaba da kawo cigaban al’umma.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel