Hukumar Hisbah ta Sokoto ta kama wani mai garkuwa da mutane

Hukumar Hisbah ta Sokoto ta kama wani mai garkuwa da mutane

Hukumar Hisbah ta jihar Sokoto ta ce ta kama wani mai yin garkuwa da mutane matukin Keke Napep mai shekaru 27

-Haka zalika, hukumar ta kama wani dan fashi da wasu karuwai shida ciki hada matan aure guda uku

-Hukumar ta ce ta gudnar da wannan kamen ne don su godewa Allah akan nasarorin da hukumar ta samu tun bayan kafa ta shekaru biyar da suka wuce

Hukumar Hisbah ta jihar Sokoto ta yi nasarar damke wani direban Keke Napep, mai suna Bashar Bello dan shekarar 27 da haihuwa, a bisa zarginsa da yin garkuwa da wasu kananan yan mata guda biyu.

Daya daga cikin yan matan biyu na da shekarar 13 dayar kuma nada 14, inda a halin yanzu suna a hannun hukumar.

Wanda ake zargin dai an kamashi ne a ranar Juma’ar da ta gabata da misalin karfe 1:00 na dare a unguwar kwannanwa.

Babban kwamanda na hukumar ta Hisbah, Dr. Adamu Bello Kasarawa, ya bayyanawa yan jarida cewa wanda ake zargin ya amsa laifinsa kuma ya ce shi ma wani ne ya saka shi amma har a lokacin bai fadi wanda ya saka shi ba.

KARANTA WANNAN: Femi Gbajabiamila zai kai ziyara zuwa Borno da Zamfara - Majalisa

Kwamanda ya ce “Ya sayi ruwan leda daga hannun wadanda ya sace a kasuwar daji bayan nan sai ya ce zai kaisu gida, amma bayan sun shiga keke Napep din sai su ka rasa inda kansu yanke.”

“Da farko ya kaisu wani otal ne da ke a unguwar tsohon filin tashin jirgin sama, inda wanda ya sanya shi yake, amma sai bai tarar da shi ba, sai ya yanke shawarar ya nemi shi a wani wurin amma sai dubunshi a cika, mutanen mu suka kamashi a lokacin da suke zagaye a kwannanwa da misalin karfe 1:00 na daren ranar Juma’a.” A cewar Kasarawa

Kwamandan ya ce zasu mika shi ga hukumar yan sandan cikin gida (DSS) don a cigaba da bincike.

Ya ce hukumar ta kuma kama wasu karuwai guda shida ciki harda matan aure guda uku. Ya bayyana cewa daya daga cikin matan auren na dauke da cuta mai karya garkuwar jiki (AIDS) kuma sun kira iyayensu sun fada masu cewa sun kama su.

Kasarawa ya kuma bayyana cewa sun kama wani Shafi’u Ibrahim da ake zargi da laifin aikata fashi da makami. Ya bayyana cewa sunyi wannan kamen ne a wani aiki da suka fita mai suna “Operation Godiyan Allah” don su gode ma Allah akan nasarorin da hukumar ta samu tun bayan kafa ta shekaru 5 da suka wuce.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: