Shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin Sokoto yayi nasara a kotun zabe

Shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin Sokoto yayi nasara a kotun zabe

Kotun sauraran kararrakin zabe dake zama a Sokoto, tayi watsi da karan da ke kalubalantar nasarar Shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar, Bello Isa Ambarura a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 9 ga watan Maris, 2019 a mazabar Illela.

Dan takaran jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben, Hon Dayyabu Adamu Kalmalo, ne ya shigar da karan akan Ambarura na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Kalmali yayi zargin cewa zaben a cike da rashin bin doka, inda ya kara da cewa zaben ba karbabbiya bace saboda tana cike da magudi.

Kalmali har ila yau yayi ikirarin cewa mafi kasarin masu zabe ba Ambarura suka zaba ba.

Yayin da yake gabatar da hukuncinsa a ranar Alhamis, 19 ga watan Satumba, Justis I. Iwodi ya bayyana cewa shaidun da masu karan suka gabatar sun gaza kawo kwakkwaran hujja sai dai ance-ance.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Majalisa ta bukaci CBN ya dakatar da sabon tsarin zaftare kudi daga masu ajiya

Yace masu karan sun gaza tabbatar da zarginsu a fiye da tunani a gaban kotu. Mai shari’an ya kuma bayyana cewa masu karan sun gabatar da zantuka ne daga ance-ance a matsayin shaidu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel