Innalillahi wa’inna illaihi ra’ji’un: Yan bindiga sun kashe mutane sama da 20 a Sokoto

Innalillahi wa’inna illaihi ra’ji’un: Yan bindiga sun kashe mutane sama da 20 a Sokoto

Rahotanni sun kawo cewa wasu da ake zargin yan bindiga ne sun kashe sama da mutane 20 a kauyen Dan Tatsako da ke karamar hukumar Goronyo na jihar Sokoto.

Wata majiya a karamar hukumar tace makasan sun iso kauyen da dare dauke da muggan makamai sannan suka fara harbi ba kakkautawa.

Yace baya ga mutane ashirin da suka kashe, yan bindigan sun lalata gidaje da sauran kayayyaki.

Yayi bayanin cewa wadanda suka tsira daga harin sun gudu sun bar kauyen domin neman mafaka a garuruwan da ke kusa da su a yankunan Goronyo da Isa da ke Sokoto.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Sokoto, Mohammed Sadiq wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, yace ba a riga an san yawan mutanen da suka mutu ba.

KU KARANTA KUMA: Da zafi-zafi: Shugaba Buhari ya bude taron hukumomin tsaro na sirri na nahiyar Afirka a Abuja

A wani laarin kuma mun ji cewa wani kwamandan rundunar soji da karin wasu dakarun sojoji a kalla 20 sun mutu sakamakon wani harin kwanton bauna da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai musu a jihar Yobe.

Mayakan sun kai wa tawagar sojojin harin kwanton baunar ne a hanyarsu ta zuwa wani sansanin sojoji da ke Benisheikh bayan sun dawo daga Borogozo, inda rundunar soji 29 ke da sansani.

Wata majiyar soji a hedikwatar rundunar soji ta 'Ofireshon Lafiya Dole' ta shaida wa jaridar 'The cable' cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:00 na yammacin ranar Laraba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel