Cikin Hotuna: Sanata Ahmed Lawan ya halarci daurin auren dan Sanata Kabiru Gaya a jihar Sakkwato
A ranar Asabar 27 ga watan Yulin, birnin Shehu wato jihar Sakkwato, ya tumbatsa da manyan kasar nan a wajen halartar daurin auren dan wakilin shiyyar Kano ta Arewa a zauren majalisar dattawa, Sanata Kabiru Gaya.
Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan, na daya daga cikin manyan baki da suka halarci wannan dauri aure tare da 'yan tawagar da aka kulla a tsakanin Khalil Kabiru Gaya da kuma amaryar sa, Fatima Umar Ajiya.
Sauran manyan bakin sun hadar da shugabnan kamfanin man fetur na kasa NNPC, Mele Kolo Kyari, shugaban hafsin sojin sama, Air Marshal Sadique Abubakar da kuma Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje tare da mataimakin gwamnan jihar Sakkwato, Manir Dan'Iya.
Tawagar shugaban majalisar dattawa da ta iso birnin Shehu cikin jirage kimanin goma ta hadar Sanata Adamu Aliero, Sanata Kashim Shettima da kuma Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko.
Yayin gabatar da jawabai, Sanata Gaya ya yi godiya ga wadanda suka samu damar amsar goron gayyatar sa tare da fatan Mai Duka ya mayar da kowa gida lafiya.
Ya kuma kwarara godiya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya turo wakilan sa tare da kyautata masa zato a kan magance duk wani kalubale da kasar nan take fuskanta.
KARANTA KUMA: Jami'ar birnin Landan ta karrama Sarki Muhammadu Sanusi II
Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng